
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Sakamakon rashin cike ƙa’idojin babbar kotun jihar Kano da hukumar hana yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, EFCC ta yi, an samu tsaiko kan sauraron ƙarar da aka shigar kan kare ƴancin shugaban jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai.
Jaridar ‘Daily Trust’ ta ruwaito cewa, waɗanda su ka shigar da ƙarar sun haɗa da; NNPP, Dakta Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Cif Clement Anele, Ledi Folshade Aliu, Buba Galadima da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso kan hukumar EFCC.
A yayin da aka tada batun, lauyan da ya karɓi shigar da ƙarar, Robert Hon, ya ce a shirye su ke domin cigaba da sauraron ƙarar.
Ganin cewa EFCC ta gaza shigar da takardar amsawar ƙarar, Robert ya buƙaci kotun da ta ƙi karɓa idan sun shigar da ita daga baya kasancewar ba su bada ƙwararan dalilan da su ka hana su yin hakan ba, tare da ɗage ƙarar zuwa wani lokaci.
A gefe guda, lauyan ɓangaren EFCC, Idris Ibrahim Haruna ya nemi kotun ta dage sauraron ƙarar domin bai wa ɓangarensa damar shirya takardar amsa wa ƙarar.
Mai Shari’a Yusuf Ubale Muhammad, wanda shi ne mai hukunci kan ƙarar, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 24 ga watan Oktoba.
Haka nan, kotun ta sanya iyaka wa EFCC wajen dakatar da ita daga keta haƙƙi, kamawa ko cin mutuncin Kwankwaso da sauran mutanen da lamarin ya shafa har sai ta yi hukunci.
