
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaba Brice Oligui Nguema na ƙasar Gabon ya gayyato shugaban kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote zuwa ƙasarsa domin ƙulla harkar kasuwanci a ɓangarorin siminti da taki musamman domin haɓaka harkar noma.
A lokacin ziyarar, Ɗangote ya gana da Shugaba Nguema da wasu manyan jami’an gwamnati inda su ka tattauna kan batutuwan sanya hannun-jari. A zaman, an mayar da hankali ne kan yadda masana’antun Ɗangote zasu taimaka wajen haɓaka tattalin arziƙin Gabon ta hanyar samar da masana’antun siminti da taki musamman a ɓangaren samar da albarkatun noma.
Nguema ya bayyana jin daɗinsa game da haɗa hannu da hamshaƙin ɗan kasuwar, yana mai cewa ƙasarsa ta na ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau ga masu son zuba hannun-jari daga ƙasar waje.
Ya ƙara da cewa, haɗa hannu da Ɗangote a kasuwanci zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, sauyawar fasahar zamani da kuma bunƙasa ƙarfin masana’antu.
Haka kuma, kasancewar Ɗangote ya yi nasara a kasuwanci da dama a Afirka, hakan ya nuna ƙoƙari da kamfaninsa ke yi don ganin an samu cigaba a ɓangaren tattalin arziƙin nahiyar.
Ɗangote ya ƙara da cewa, haɗakar ɓangarorin biyu ta nuna ƙara faɗaɗa da mamayar da masana’antunsu ke yi tare da taimaka wa ayyukan cigaba a Afirka.
