Tsadar rayuwa: Mun janye daga zanga-zangar da muka ƙirƙiro – Murtala Gamji

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Majalisar Matasa na Nijeriya, Kwamared Murtala Muhammed Garba wanda aka fi sani da Murtala Gamji, wato jigon da ya yi tunanin ƙirƙiro da zanga-zangar da ake shirin yi ƙarshen wannan watan nan akan tsadar rayuwar da al’ummar ƙasar ke fama da ita ya ankarar da al’umma wata mummunar manufa da wasu mutanen Kudancin ƙasar ke da shi akan zanga-zangar.

Gamji ya ce sun ƙirƙiro da zanga-zangar ne domin kira ga gwamnati ga alhalin da ‘yan ƙasa ke ci akan tsadar rayuwa, harkar tsaro da sauran matsaloli da suka yi wa Nijeriya katutu, inda ya ce kuma sun samu goyon baya daga manyan mutane ciki har da Kudancin Nijeriya.

To sai dai daga bisani Gamji ya ce sun gano ana so a yi amfani da zanga-zangar ne wajen shigo da wata mummunar manufa domin ruguza yankin Arewa, domin a cewarsa wani shugaba a Nijeriya ya umarce su da ya tattaro masa matasansu 23 ya ɗauki nauyin kuɗin jirgi zuwa Fatakwal domin su tattauna da shi akan zanga-zangar, inda bayan sun kwana a Fatakwal a cewarsa sai mutumin ya sake ɗaukarsu zuwa Jihar Delta, suka yi kwana shida.

“Saboda haka yanayin maganganunsu da abubuwan da suke so mu yi a wajen zanga-zangar sai jikinmu ya yi sanyi, muka ce to ai mu manufarmu daban da ta waɗannan mutanen.

“Su nasu mun yi nazari kuma mun yi tunani kamar akwai lauje cikin naɗi, domin suna so mu yi abin a Jos, Kaduna da Abuja, kuma mu tottoshe hanyoyi, wanda mu ba manufarmu kenan ba.

“Saboda haka yana cikin abin da ya sa muka yi tunani da sauran manyanmu muka ce musu mu ba za mu yi wannan zanga-zanga ba,'” inji Gamji.

Ya jaddada cewa manufarsu ta shirya wannan zanga-zanga shi ne domin su nuna wa gwamnati halin da ake ciki a ƙasar, amma su kuma ‘yan Kudancin ƙasar manufarsu daban.

“Kalamansu tabbas sun ba mu tsoro, domin suna faɗa mana yawan sojoji da ‘yan sandan da ke cikin garin Abuja da cikin Fadar Shugaban Ƙasa, suna cewa ka da mu damu za su ɗauki nauyin komai, kuma za su sa waɗansu su bi mu.

“Saboda haka a taƙaice mu ba za mu yi ba, mun janye.

“Kuma hatta maganganunsu suna cusa mana ƙin jinin manyanmu da sarakunanmu da malamanmu da sauran jagororinmu na siyasa.”

Gamji ya ƙara da cewa akwai yunƙurin shigo da wasu gurɓatattun mutane domin su dagula zanga-zangar zuwa wata manufa tasu ta daban, kamar yadda ya bada misali a Jos lokacin da a ka yi zanga-zangar EndSars, inda wasu gurɓatattu suka shigo ciki aka fara ƙone-ƙone da rikicin ƙabilanci da addini.

Kwamared Gamji ya yi kira ga matasa cewa zanga-zangar da za a fito a yi ba irin wadda suke so a yi ba ce, inda ya ce su zanga-zangar da suka shirya ta soyayya ce, ta zaman lafiya ce kuma ts dimukraɗiyya ce da gina Arewa tare da soyayyar juna, “domin kokenmu muke so mu kai wa Bola Ahmed Tinubui,” inji shi.

A ƙarshe ya roƙi gafarar malaman addini da su yi haƙuri a bisa munanan kalamai da matasa suka dinga furtawa a kansu yayin da suke nusan da al’umma akan illolin zanga-zanga da haramcinta a addinin Musulunci.

Kwamared Murtala Gamji shi ne wanda ya jagoranci zanga-zanga da fafutikar ganin an saki  Hamza El-Mustapha a lokacin da yake tsare a kurkuku.

By ukarofi