Lokpobiri ya sasanta Ɗangote da NNPC

Spread the love

Sanata Heineken Lokpobiri, ƙaramin Ministan Man Fetur ya kira wani babban taro na masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da iskar gas domin warware matsalolin da suka taso tsakanin Ɗangote da Gwamnatin Tarayya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Nneamaka Okafor, mai baiwa ministan shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa ta fitar.

Taron wanda aka gudanar a ranar Litinin a Abuja ya samu halartar Alhaji Aliko Ɗangote, Mista Farouk Ahmed, Shugaban Hukumar,NMDPRA.

Sauran sun haɗa da Mista Gbenga Komolafe, Shugaban Hukumar, NUPRC da Malam Mele Kyari, Babban Jami’in Rukunin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC Ltd.).

Idan dai ba a manta ba a baya-bayan nan ne aka samu sabani a tsakanin shugabannin kamfanonin Dangote da NMDPRA da kuma NNPC kan wasu batutuwan da suka shafi matatar man Ɗangote.

Ɗangote ya bayyana cewa yanzu kamfanin na NNPC bai mallaki kashi 20 cikin 100 na matatar man ba, yana mai jaddada cewa yanzu haka kamfanin mai na Najeriya yana da kashi 7.2 cikin 100 na matatar ne saboda rashin biyan kuɗin da ya kamata kamfanin yayi.

Sai dai kuma kamfanin na NNPC ya ce an yanke shawarar kashe kuɗaɗen da aka biya kuma aka sanar da matatar Dangote watanni da dama da suka gabata.

Hukumar ta NMDPRA ta kuma samu saɓani tsakaninta da Ɗangote kan batutuwan da suka shafi lasisi, wanda hukumar ta ce matatar ta Dangote na kan matakin fara aikin ne.

By ukarofi