
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ta musanta batun cewa ta janye daga zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shirin yi faɗin Nijeriya, ta na mai cewa ba ta ɗaya daga cikin waɗanda su ka shirya ta.
Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya bayyana haka cikin wata takarda da ƙungiyar ta fitar a ranar Talata, inda ya ce ba za su janye daga zanga-zangar da ba su suka tada batunta ba. Ya ce ƙungiyar tana da tsarinta na cikin gida game da yin hukunci kan ababan da su ka shafi al’umma cikin har da zanga-zanga.
Ya ƙara da cewa duk da ba NLC ba ce ta shirya zanga-zangar, amma ta na goyon bayan ƴan Nijeriya da ke fama da matsanancin rayuwa.
Ajaero ya kuma yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya samu damar tattaunawa da waɗanda su ka shirya zanga-zangar tare da yin duba ga buƙatunsu.
Kazalika, NLC ta yi gargaɗi kan kar a tilasta nuna wa ƴan zanga-zangar ƙarfin mulki, a madadin haka, gwamnati ta saurari kokensu tare da ɗaukar matakan da suka dace.
