Daga USMAN KAROFI a Abuja
Meta Platforms Inc, kamfanin da ke da Instagram da WhatsApp ya sanar a ranar Laraba cewa za a cire wasu shafuka 63,000 da ke da alaƙa da masu aikata laifuka ta yanar gizo a Nijeriya, waɗanda ke damfarar kuɗi a yayin amfani da shafukan.
A cikin rahoton kamfanin na 2024 a ranar Laraba, Meta ya bayyana cewa shafukan da aka cire sun kai kimanin 63,000 a yayin wani binciken haɗin gwiwa da kamfanin ya gudanar.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa ya gano tare da cire waɗannan shafuka ta hanyar amfani da fasaha na zamani da kuma cikakken bincike, ta yadda hakan ya inganta tsarin gano irin waɗannan shafukan kai tsaye.
Ya ƙara da cewa, “Mun cire kusan shafukan63,000 a Najeriya da ke yunƙurin damfarar mutane kuɗi ta hanyar yanar gizo.”
Wani babban ma’aikaci a kamfanin na Meta, Antigone Davis, ya ƙara bayyana cewa yayin da akasarin yunƙurin da aka yi ba a yi nasara ba.
“Yayin da bincikenmu ya nuna cewa yawancin waɗannan yunƙurin ‘yan damfara ba su yi nasara ba kuma galibin su ,manya aka yi yunƙurin damfara, mun ga wasu na yunƙurin kaiwa har ga yara ƙanana,” in ji Davis
Kamfanin na Meta ya bayyana cewa ƙoƙarin da ya yi ya wuce cire shafukan, yana mai cewa yana kuma aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro, da tallafawa bincike da kuma gurfanar da waɗanda a ke zargin su gaban kuliya ta hanyar amsa kiran da hukuma za ta yi ma su.
