
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kwanaki kaɗan bayan da shugaban matatar mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yi zargin cewa akwai jami’an kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC da ke da ɓoyayyun masana’antun mai a ƙasar Malta, alƙaluma sun bayyana cewa Nijeriya ta sayo man fetur na tsabar kuɗi da adadinsa ya kai Dala biliyan 2.25 daga ƙasar.
Wata sanarwa daga ‘Trade Map’, ta ce a shekarar 2023, Nijeriya ta shigo da man fetur na Dala biliyan 2.8 wanda hakan ya haura da kashi 342 a kan na Dala miliyan 47.5 da aka sayo a shekarar 2013.
An gano cewa, daga shekarar 2017 zuwa 2022, babu man fetur ɗin da aka sayo daga Malta. Duk da haka, an samu hauhawa mai yawa inda a shekarar 2023, Nijeriya ta shigo da man fetur na Dala biliyan 2.08.
Sai dai shugaban NNPC, Mele Kyari ya musanta mallakar masana’antar mai a ƙasar waje, sannan ya ce, bai san wani ma’aikatacin NNPC da ke mallakar masana’antar mai ba a Malta ko a wani wuri a ƙasashen waje.
Kazalika, ana yamutsa gashin baki ne da Ɗangote bayan da shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed ya zargi matatar Ɗangote da mallakar sinadarin ‘sulphur’ sama da yadda ake samu daga waɗanda ake shigowa da su Nijeriya inda Ɗangote ya ce hakan wani yunƙuri ne a nuna kushe matatar tasa.
