Kyakkyawar zamantakewa kaɗai za ta kawo zaman lafiya

Spread the love

A wannan mako ina son hankalin mu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautatawa juna a mu’amala ta yau da kullum ke iya haifar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a, musammam mutane masu bambancin ƙabila, addini ko ra’ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya haɗa jama’a, daga ɓangarori daban-daban.

Babu shakka zaman lafiya da jama’a, tausayawa, tallafawa, da kaucewa duk wani abu da zai iya kawo saɓani da rashin fahimta a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuƙa, babu ma kamar wannan lokaci da jama’a ke cikin ƙunci da rashin yarda da juna, saboda kurakuran da suke zargin wasu suna yi da gangan, don cimma wata manufa ta son ran su, ko danne haƙƙin wasu.

Rashin yarda, zargin juna, hassada, kishi, zalunci, babakere, da tauye haƙƙin raunana, halaye ne da aka saba gani a zamantakewa ta yau da kullum, inda wasu ke ƙoƙarin fifita kansu da tilasta buƙatun su kan na sauran mutane, a dalilin haka kuma sai a samu turjiya da nuna rashin yarda daga wani ɓangare.

Mummunar halayya irin ta hassada na ruguza imani da mutuncin mutum, saboda kasancewarta mugun ciwon da ke nuƙurƙusar mai yin ta a cikin zuciyarsa shi kaɗai.

Mun sha jin ƙorafe-ƙorafe daga mutanen da aka tauye wa haƙƙi ko aka zalunta, sakamakon son zuciyar da wani ya nuna musu, don kawai ya samu damar da zai yi abin da ya dace amma ya kasa, saboda zarmewa da son zuciya.

Akwai mutanen da za ka riƙa yi musu kallon manya ana girmama su saboda matsayin da suke da shi, ko arzikin da Allah ya ba su, har ma ka ji ana yi musu kirari, don kwaɗayin samun wata alfarma daga wajensu. Sai dai da a ce za ka samu jin abin da waɗanda ke ƙarƙashin sa ko iyalinsa suke faɗa, ba za ka so ka sake kallon sa da martaba ba. Saboda halinsa na rashin fitar da haƙƙin waɗanda suka yi masa ƙwadago da gumin su, sauke nauyin iyali da ‘yan uwa da ke kansa. Yana ganin idan ya cire wani abu daga arzikin sa to, zai rage masa jin daɗi, ko zai bayar a inda ba a san zafin su ba.

Mutane masu son zuciya ba sa taɓa samun wadata da gamsuwa da rayuwar su, ko da kuwa sun samu damar yin duk abin da suke so, saboda ko da yaushe tunanin su ba ya wuce jin daɗin kansu ta hanyar ƙuntatawa wasu.

Don haka kirana ga mai karatu shi ne a guji fifita son rai, domin an ce son zuciya ɓacin zuciya! 

Wasiƙa daga Bilkisu Adam, 08168716583.

By ukarofi