Hukumar Tace Finafinai: Yadda Abba El-Mustapha ya kawar da saɓanin siyasa a cikin Kannywood

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU KANO

A daidai lokacin da shugaban Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano Abba El-Mustapha yake cika shekara guda a kan kujerar sa wasu na ganin ya yi abin a yaba wasu kuma na ganin har yanzu kwalliya ba ta fara biyan kuɗin sabulu ba. Kan haka ne wakilinmu ya nemi jin ta bakin sa domin ya bayyana wa masu karatunmu abubuwan da suka wakana a tsawon shekara guda da ya yi. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta a kasance.

MANHAJA: A yanzu ka samu tsawon shekara guda a kan wannan kujerar ta shugabancin hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano, don haka masu karatunmu za su so jin yadda ka gudanar da aikinka a tsawon shekara guda da kama aiki.

ABBA EL-MUSTAPHA: To Alhamdulillah, yau mun shekara guda a kan wannan kujerar ta shugabancin Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano wadda maigirma zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bani ragamar kuma ya sahale mini cewar na jagoranci ita wannan Hukumar, kuma Ina ganin ba wai don na isa ba ko don na fi kowa ba, sai don yana ganin za a samu canje-canje kuma za a samu irin abubuwan da ake so a samu daga gare ni, don haka ina yi masa godiya da wannan damar da ya bani kuma ina godiya ga dukkan waɗanda suka ba mu goyon baya a kan wannan aikin da muka yi na shekara guda. Domin wasu da suke a gaba gaba wajen ba mu goyon baya za ka ga ba ma ‘yan jam’iyyar siyasar mu ba ne, haka aka kawar da bambancin siyasa aka zo aka rungumi juna ake ta yi mini fatan alheri tare da ba ni haɗin kai da kuma shawarwari da ƙwarin gwiwa kan duk yadda za a yi a ga an kai ga samun nasara.

To a lokacin da yake kai sabon zuwa ne. Ko a yaya ka samu wannan hukumar?

E to ita wannan Hukumar tace finafinai da ɗab’i na zo ta ne a matsayin baƙo saboda gudanar da mulki zan yi. Amma na zo mata a ɗanta, musamman da yake na fito daga cikin ‘yan fim a matsayina na jarumi a masana’antar Kannywood kuma furodusa, don haka na san wasu abubuwan da suke faruwa a cikin ta, kuma da na zo ɓangaren gudanar da mulki na duƙar da kaina saboda na samu jajirtattun ma’aikata a wajen, sai na zamar musu almajiri wajen neman na san wasu abubuwan da nake so na sani domin na samu damar yin ayyukana a cikin tsari. Kuma suka koya mini aiki, kuma Alhamdulillah, idan ka duba za ka ga na shigo cikin gidan a lokacin yana tare da ƙalubale kala-kala. To amma cikin ikon Allah a shekara guda abubuwa duk sun saitu, kuma da dama suna alfahari da ganin yadda hukumar ta jajirce wajen ganin ta fitar da duk wasu abubuwan da ba su dace ba tare da tsaftace kalamai da kuma gyara abin da ake ganin ba daidai ba ne a cikin masana’amtar Kannywood.

Kuma ita wannan hukumar ba wai a kan harkar fim kaɗai huruminta ya tsaya ba. Ka ga akwai harkar rubutu, hotuna, masu maganin gargajiya, amma su babu ruwan mu da yadda suka samar da maganin su, amma yadda suke tallan maganin nasu a nan muke da hurumi kamar nuna hoton tsiraici da kalamai na batsa da suke yi, don haka dole sai mun duba wanne irin rubutu suka yi a jikin kwalin maganin nasu. To ta nan muka shigo ciki, kuma kowa ya ga yadda muka yi wajen bayar da gudunmawa don ganin an tsaftace harkar, wanda a baya har ba ka iya shiga kasuwa sai an dame ka da irin wannan kalamai na batsa, amma yau ka na gani abin ya zama tarihi a Kano.

Bayan wannan akwai harka ta masu gidajen daɓe, su ma a ƙarƙashin Hukumar tace finafinai da ɗab’i suke, da masu gidajen kallo da sinimomi , duk a ƙarƙashin Hukumar tace finafinai da ɗab’i suke har ma masu buga takardu da masu ɗaukar hoto da masu zane-zane da mawaƙa, kuma duk muna shiga cikin al’amuran domin mu ga an samar da ci gaba. Don yanzu idan ka ɗakko harkar rubutu za ka ga har gasa muka saka, wadda muka yi hakan domin mu tayar da su daga bacci da su marubuta suka yi, kuma harkar rubutu musamman a Jihar Kano za ka ga ba a shiga ana shirya gasar, don haka da na zo aka ce wannan hukumar ba ta taɓa shirya gasar marubuta ba. To a yanzu mun shirya har ma akwai wani tagomashi da mutum zai samu, na ɗaya zai samu dubu ɗari biyar na biyu dubu ɗari uku na uku zai samu dubu ɗari biyu.

 Kuma wanda duk ya shiga har zuwa na hamsin kowa zai samu tagomashi. Don mu abin da muke so shi ne mu dawo da karsashin yin rubutun yadda za a dawo ana yin rubutun al’ada da sauransu. Kuma wannan abin zai ƙara wa harkar rubutu ƙaimi da daraja a duniya wanda za su tabbatar da cewa ana kula da su ana ba su goyon baya. 

Bayan wannan idan aka gama za mu zo mu yi taron horaswa da sauransu.

Su kansu harkar fim za a ga yadda muka shiga cikin abubuwan su, don idan an duba za a ga kamar gidajen da ake yin wasannin daɓe ana ta ƙorafi a kansu, amma da muka shiga cikin lamarin muka janyo su muka nuna musu ga abubuwan da ake so ku yi ga wanda ba a buƙata. Kuma har gasa muka saka musu kuma manyan masu muƙamai ne ma a cikin gwamnati suka halarci wajen don su gane wa idonsu yadda aka tsaftace harkar.

Akwai kuma abubuwa da dama da muka gudanar, kamar yanzu muka shiga harkar masu adaidaita sahu domin kula da yadda suke saka hotuna da zane wanda ba daidai ba ne irin su kwarangwal da na shaye-shaye da sauransu, to mun shiga ciki, kuma za mu fara kamawa muna kai su gaban alƙali, saboda muna son idan baƙp ya shigo cikin Jihar Kano ya ga tarbiyya a bayan Adaidaita Sahu ba hotunan batsa ba . Don haka a wannan gaɓar muke neman haɗin kai na al’umma don ba za mu iya ba sai da haɗin kansu.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

By ukarofi