Kaucewa nuna wariyar addini da ƙabilanci

Spread the love

Assalam alaikum. Barka da wannan lokaci. Ina yi wa duk ma’aikatan jaridar Blueprint Manhaja barka. Allah Ya ƙara basira da hikima.

Sanannen abu ne kasancewar Nijeriya ƙasa mai yawan ƙabilu. Tana da al’adu da dama da ƙabilu iri-iri, abin da har ake ƙiyasin akwai yaruka fiye da 400 da ƙabilu fiye da 350. Lura da irin waɗannan bambance-bambance, lallai abu ne mai matuƙar wuya tafiyar da su a dunƙule. 

Tun bayan da Nijeriya ta koma tubar dimukraɗiyya a 1999, gwamnatocin baya da aka yi sun yi ta ƙoƙarin ganin sun haɗe kan al’ummar ƙasar a matsayin ƙasa ɗaya al’umma ɗaya. Sai dai cimma nasara wajen tabbatar da wanzuwar taken ƙasar na, haɗin kan mabambantan jama’a, ya zama tamkar mafarki a yanayin da ƙasar ke ciki, da kuma yadda al’ummar ƙasar suke kallon junan su. 

Nuna bambance bambancen addini da ƙabilanci da ya yi yawa a ƙasar ya mayar da ƙasar wajen da shugabanci ya ke da wuyar sha’ani. Yanzu haka a yanayin da mafi akasarin jihohin Nijeriya ke ciki, nazari kan sasanta rikice-rikice ya wuci batun wani Kwas da mutum zai je jami’a ya karanta don a ba shi shaidar kammalawa. Da dama daga cikin Gwamnonin ƙasar nan, yau da gobe ta sa sun zama masana warware saɓani da rikice-rikice a jihohin su, sakamakon irin yadda faɗace-faɗace masu nasaba da addini da ƙabilanci suka yi yawa a jihohin nasu. 

Wannan hali da ake ciki ne ya haifar da yanayin siyasar da yanzu ake gani a ƙasar, siyasar addini da ƙabilanci. Ya zama dole a faɗi gaskiya, wannan mummunan yanayi ya haifar wa ƙasar koma baya mai yawa. Shi ya sa dole a ja hankalin matasan ’yan siyasa masu tasowa su fahimci irin haɗarin da ke fuskanto su, a matsayin su na manyan gobe, domin samar wa ƙasar makoma tagari.

Zan kammala da gargaɗin duk wasu da za su yi ƙoƙarin kawo wa al’umma wani mugun ra’ayi da zai ruguza kyakkyawan tarihin da suke da shi tun iyaye da kakanni na son juna da haɗin kai su kiyayi kansu daga wannan mugun tafarkin da suke shirin jefa kansu. Tsawon shekaru yankin da al’ummarsa ya zama wajen da jama’a da dama ke sa masa ido, kuma ake kishin sa. Bai kamata mu bari wani ko wasu su zo su lalata mana wannan kyakkyawar shaidar ba. Ya kamata su ɗauki misali daga abin da ke faruwa a makwabciyar Jihar Bauchi wato Filato, inda siyasar ƙabilanci da wariyar addini ya ke jefa jihar da al’ummar ta cikin wani yanayi mawuyaci na taɓarɓarewar tsaro da zaman lafiya.

Allah Ya ba mu zaman lafiya a Nijeriya, Ilahee.

Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, Kaduna. 08168716583/07014606518.

By ukarofi