Dangote a hannun azzalumai

Spread the love

Dangote ya kashe sama da dala biliyan ashirin wajen gina matatar mai a ƙasarsa Nijeriya don ya samawa mutane aikin yi da kuɗin shiga sannan a sauƙaƙawa ’yan ƙasa wahala da tsadar mai. Sai dai manyan ma su iko da ƙasa, azzalumai maƙiya Allah sun hana matatar man aiki ta hanyar daƙile duk wata hanya da ya ɗauko na fara aikin da kuma ƙaƙaba ma sa sharri iri-iri.

Wannan duk saboda idan har aka fara aikin kuɗaɗen da suke samu ta hanyar haram wajen shigo da mai daga waje zai tsaya, sannan wasu sun nemi dole sai ya ƙara wasu kuɗi akan yadda ake sayar da ɗanyen mai kafin a fara ba shi (ma’ana sai ya saya fiye yadda suke sayarwa a wajen ƙasar). A baya har Dangoten ya yi tunanin rabuwa da ɗanyen man Nijeriya ya zaɓi ya fara shigo da man daga waje, duk saboda munafurci da mugunta da ake ma sa.

Mutum ne da ya ke da damar gina rifainaren a ko ina a duniya amma ya zaɓi ya gina a ƙasarsa amma kuma azzaluman aasar sun hana ƙasar amfana da ma’aikatar. Wasu maganganu da ya yi a jiya sai da ya ba wa mutane tausayi. Ya ce “A yanzu fa shekaruna sittin da bakwai, uku ya rage na cika saba’in, lokaci kaɗan ya rage mini a duniya, idan na mutu ba za a binne ni da komai daga cikin abin da na tara ba, don haka ba ni da asara”. Da ya ga ba yadda ya iya da azzaluman ƙasar sai ma ya ce ya haƙura da matatar man, idan NNPC za su biya shi kudin da ya kashe wajen ginawa, ya yarda zai sayar mu su kawai ya huta. NNPC da suka kasa gyara tsoffin matatun man ƙasar nan da suka lalace shekara da shekaru.

Akwai wani Gwamna a Nijeriya da ya fallasa cewar dukkan matatun man Nijeriya guda hudu idan ka haɗa su ba su kai girman na Dangote guda daya da ya gina ba, amma kudin da aka kashe wajen gyara matatun man ya fi kuɗin da Dangoten ya kashe wajen gina nasa, amma har yanzu a durƙushe su ke ba sa aiki, sannan kuɗin da aka kashe wajen gyaran ba su ba dalilinsu. An jima ana fatan matatar Dangote ta fara fitar da mai, saboda dole zai yi sauƙi, kuma dala za ta faɗi warwar saboda mafi yawan neman dala da ake yi ya fi tafiya a safarar mai daga waje. Amma kash! Azzaluman ba za su bari talaka ya sami sauƙi ba.

Allah kaɗai ya san yaushe Nijeriya za ta gyaru.

Daga YAKUBU M. KUMO.

By ukarofi