Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Talatar da ta gabata ne jam’iyyar All Progressiɓes Congress ta yi watsi da raɗe-raɗin da ake yi cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike na yin tasiri a kan hukuncin da jam’iyyar reshen jihar Ribas ta ɗauka.
Jam’iyyar ta musanta raɗe-raɗin, inda ta ce tsohon gwamnan Ribas ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, kuma ba ya halartar duk wani taron su na siyasa.
Da yake jawabi ga manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja, Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC na Ribas, Cif Tony Okocha, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da aka yi na ganin Wike ya koma jam’iyyar, sun gamsu da cewa ministan babban birnin tarayya zai ci gaba da kasancewa ɗan jam’iyyar PDP.
Ya ce: “Lokacin da na ji haka, sai na yi dariya saboda Wike ɗan PDP ne. Muna nan APC. Shin akwai wanda zai iya cewa saboda Mista Wike minista ne a gwamnatinmu ta APC, ya kamata mu yi ta fama da shi?
“Wike baya halartar taronmu. Na yi muku bayani a nan. Mun yi taro da masu ruwa da tsaki, amma Wike bai taɓa halartar wurin ba. To a wane lokaci ne yake yin tasiri a APC a jihar Ribas? Tasirinsa, kamar yadda kuka sani, shi ne saboda yana minista a ƙarƙashin gwamnatin APC. Don haka ba za mu iya zama cikin ƙiyayya da shi ba. Amma a ce yana rinjayar mu, ta yaya? Yana biyan kuɗinmu ko kuma yana halartar taronmu? Amsar ita ce a’a.”
A ci gaba da, Okocha ya kuma bayyana dalilin da ya sa babu wani daga sansaninsu da ke kiran tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin mamba.
Sai dai tsohon gwamnan ya nisanta kansa daga harkokin jam’iyyar tun lokacin.
Sai dai shugaban jam’iyyar APC na Ribas ya bayyana cewa Amaechi ya gargaɗi sakatariyar jam’iyyar na jihar da kada ya sake yi masa goron gayyata ga duk wani taro.
“A kan batun Ameachi, ba ni da wata tambaya da zan amsa. Ni ne shugaban ma’aikata ga Rotimi Amaechi. Ka tuna cewa a wani lokaci, ya shiga makarantar lauya kuma daga wannan shekara. Har ila yau, kuna sane da cewa bayan zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ya ɓace.
“Don haka ko shi dan jam’iyya ne ko a’a, ba zan sani ba saboda a duk taron da muka kira bai fito ba. Bari in baku misali da taron da muka kira ga ɗaukacin tsofaffin gwamnoni da ministoci, shi (Amaechi) ya aike da saƙo ga sakataren jam’iyyar ya kuma gargaɗe shi da kada ya kuskura ya sake tura masa sako game da jam’iyyar.
“To, idan kun haɗu da shi, ku tambaye shi inda yake. Amma ni, ban san inda yake ba,” ya bayyana.
