Burin kyautata ci gaban al’ummar Fagge ya sa na amsa kiran tsayawa takara – Aliyu Sanata 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ɗaya daga masu neman tsayawa takarar shugabancin Ƙaramar Hukumar Fagge a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP, Hon. Aliyu Tijjani Inuwa da ake yi wa laƙabi da Sanata, ya ce sakamakon tafiyar su ta Kwankwasiyya an sha tiri-tiri shekara takwas har aka kai ga samun nasarar a zaɓe ba shi da niyyar yin wata takara sai da jama’a suka yi ta kiraye-kirayen ya fito takara.

Ya ce  ganin al’umma sun nuna cancantarsa na ganin zai aikata abinda ya dace a ƙaramar hukumar Fagge domin shi tun babu gwamnati ko wani muƙami yake abinda masu muƙami a tsohuwar gwamnati ba sa iya yi wajen kula da al’umma, wannan kira da ya yi yawa tasa bayan tuntuɓa na magabata da abokan da ‘yan’uwa ya amince ya fito neman tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukumar Fagge.

Hon. Aliyu Tijjani Sanata ya ƙara da cewa ya amsa fitowa neman takarar ne domin ta yiwu tanadi ne Ubangiji ya yi masa da bai sani ba, saboda bakunan jama’a ba a san albarkar bakin wani ba, duba da irin abubuwa na tallafawa cigaban al’umma da yake yi.

Ya ce cikin irin abubuwa da yake akwai tallafi da yake yi wa ɗalibai na biya musu kuɗin makaranta da na jarabawa har ma na zirga-zirga na waɗanda ke jami’o’i da makarantun sakandare. Akwai waɗanda ake tallafawa da jari da kuma ƙoƙari na kawar da matasa daga shaye-shaye da sama musu sana’o’i da yawa ya kai wasu suna harkar kasuwa a inda yake.

Ya ce ko a tsarin jam’iyya shi ya taɓa kamawa jam’iyya ofis a Fagge Kuma duk zagayen da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a dukkan ƙananan hukumomi 44 ya na ɗaukar nauyin motocin  matasa da abinci da ‘yan kuɗin buƙata da ake bayarwa. Suma dattawa yankin da makarantun Islamiyya  da masallatai ana tallafawa bukatunsu haka  mata masu ƙananan sana’oi ana basu jari , marasa lafiya da ake rubuta musu magunguna in sun je asibiti sun ga likita sukan zo a saya musu magunguna.

Hon. Sanata ya ce bai amince da fitowa takara ba saida ya bibiyi matsaloli da sanin buƙatun ƙaramar hukumar Fagge ta yadda za su ɗauki mataki na warware matsaloli da kuma biyan buƙatun al’umma idan an kai ga nasara.

Ya ce ita Fagge a matsayinta ta ƙaramar Nijeriya da take da ƙabilu da suke zaune a wani sashe na yankinta za su yi ƙoƙarin basu kulawa domin gwamnatoci a baya ba su fiye yi musu ayyuka ba ya lura a yankunan da suke suna da matsalar magudanan ruwa da lalacewar tituna da rashin wadataccen lantarki duk kuwa da cewa akwai shugana na Kasuwanci da suke da yake  taimakawa samun kuɗaɗen shiga, suna da buƙatar inganta tsaro, za su tsaya su bada kulawa a kyautata musu.

Ya ce za su samar da tsari na kyautata tsaftar muhalli da yashe magudanan ruwa akai akai da kula da  gyaran fitilun unguwanni da suke lalacewa da sanya wasu a Fagge  za a samarda ma’aikata da za su riƙa kula da gyaran magudanan ruwa da sama musu kayan aiki suma jama’a a wayar musu da kai kan kulada tsaftar muhalli da Samar da   kwandon zuba shara a wurin sana’o’i domin ƙarfafa gwiwa.

Hon. Aliyu Tijjani Inuwa Sanata ya yi nuni da cewa Fagge na da kasuwanni da suke kewaye da ita za su yi amfani da abinda ake samu daga garesu wajen bada tallafin Ilimi ga matasa dake manyan makarantu da kuma tallafawa sana’oi za su zauna da masu ruwa da tsaki a fannin Ilimi yan asali yankin a riƙa tsara yanda za a tallafawa  cigaban ilimi hakan zai taimakawa tsarin Gwamnatin Kano na ilmi kyauta sannan a samarwa al’ummar Fagge musamman matasa damar amfana da kasuwanni da ke kewaye da ita.

Ya ce ƙaramar hukumar Fagge sun fi ƙarfafa akan harkar Kasuwancin Babura da gyaransa da ɗinki zai zo da tsari na tallafa musu da zamanatar da tsarin ɗinki da za a rika fitar da kayanda ake ɗinkawa  ƙasashen duniya. Sannan zai tallafawa ƙoƙarin ɗan majalisar su na jiha Tukuru Muhammad da ya kai ƙuduri majalisa akan a daina sayar da gidaje zaman al’umma ana mayar da su manyan shaguna a ƙwaryar Fagge domin hakan barazana ce da za ta gurgunta tarihin Fagge, za su haɗa kai da jagorori da masu unguwanni a dakatar da hakan.

Hon. Aliyu Sanata ya yi kira ga al’ummar Fagge su ba shi haɗin kai da goyon baya da kuma  taya shi da addu’a idan Allah ya ba shi dama na zama shugaban ƙaramar hukumar Fagge ya yi riƙo da hannunsa wajen kyautata ci gaban al’umma.

By ukarofi