An cafke ɗan majalisa, tsohon ciyaman da hakimi bisa zargin garkuwa da mutane a Zamfara

Spread the love

Wani ɗan majalisa da ke wakiltar ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara ya faɗa hannun ‘yan sandan Jihar Zamfara bisa zargin hannu da ya ke dashi a garkuwa da mutane.

Kwamishinan ‘yan sanda na Zamfara, CP Muhammad Shehu Dalijan ne ya bayyan haka a wata tattaunawa da yayi.

Ya bayyana cewa akwai Hakimin Kaura Namoda, Alhaji Jafaru Abdullahi da kuma tsohon ciyaman na Kaura Namoda, Nasiru Muhammad bisa zargin garkuwa da mutanen.

Hakiman Bukuyum, Danjibga da Unguwar Gyauro waɗanda ke ƙananan hukumomin Tsafe da Bukuyum suma ana zargin su a laifin da aikata.

Bincike ya fara nuna Hakimin Kaura Namoda ya haɗa baki da masu garkuwa Alhaji Bala da Hali Sidi a kayi garkuwa da mutane tara a ƙauyen Gidan Sambo da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda.

Kwamisshinan ya bayyana cewa su ukun sun amshi ₦800,000 a mastayin kuɗin fansa kafin a saki mutanen.

Haka suma hakiman Danjibga,Umguwar Gyauro da Bukuyyum za su fuskanci tuhuma wajen kwamitin da gwamnatin jihar ta naɗa domin amsa tahume-tuhume kan zargin garkuwa da mutane.

‘Yan sanda sun gudanar da bincike mai zurfi wanda har sun miƙa rahoton ga gwamnan jihar.

By ukarofi