Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministar Harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta yi zargin cewa akwai wasu ƙososhin gwamnati da suka takura mata.
Ministar Matar ta yi zargin cewa ana takura mata ne saboda ta ƙi sanya hannu kan buƙatar karɓo bashin dala miliyan 500 daga Bankin Duniya.
Hakan na zuwa ne kwanaki bayan kwamitin Majalisar Wakilai ya titsiyeta kan zargin karkatar da Naira Biliyan 1.5.
Ministar ta yi wannan zargin ne yayin wata hira ta wayar tarho da manema labarai.
Ta ce, “Akwai bashin dala miliyan 500 da ya kamata na sanyawa hannu, amma na ƙi sanyawa. Akwai kuma wani tun da farko na dala miliyan 100.”
“Dukkanin basussukan da suke karɓa ciki har da na Bankin Duniya da sauransu, ko kun san cewa ma’aikatan bankin duniyan a Nijeriya suna karɓar kaso 40?”
“Waɗannan mutanen ya kamata ku sanyawa ido. Ya kamata ku gano inda matsalar take sannan su barni na huta.
“Yanzu rayuwa ta na cikin hatsari saboda na ƙi sanya hannu kan bashin na dala miliyan 500. Bari na gaya muku wani abu, idan na sanya hannu kan bashin nan zan samu kaso 5 bisa ɗari, amma na ƙi sanyawa.
“Wannan na daga cikin dalilin da ya sanya majalisa da dukkaninsu suka taso ni a gaba,” inji Uju Kennedy-Ohaneny.
