Aman jini

Spread the love

A da can, sai dai na ji labarin aman jini, amma yanzu kasancewa ta a fagen lafiya dumu-dumu, na ga aman jini da ido na kuma na karanta shi. 

Aman jini zai iya kasancewa jinin ne tsurarsa, wato jini ja-jawur. Zai kuma iya kasancewa jini ne mai haɗe da abinci, wanda launinsa kamar kofi (coffee) ne ko na ce launin shayi ruwan bunu. 

Aman jini alama ce da ke nuni da cewa, mutum yana zubar da jini daga ciki. Ta iya yiwuwa jinin daga jannai yake fita ko daga tumbi ko kuma daga farkon sashen ƙaramin hanji. 

A na yin gwajin ‘endoscopy’, domin a ga wai daga ina jinin yake fita. Gwajin ‘endoscopy’ ana sanya wata ’yar ƙaramar kyamara ne a bututun abinci, wacce za ta haska wa likita, domin ya ga daga ina jinin ke fita. 

A mafi yawan lokaci, aman jini yanayi ne da ke buƙatar agajin gaggawa daga malaman lafiya.

A wasu lokutan kuma, amai mutum zai yi mai ƙarfi, wanda zai ga ɗigo-ɗigo na jini a ciki. Shi wannan na nuna cewa, an samu ciwo ko yagewa da rauni a bututun abinci a yayin da aman ya ke giftawa da gudu kuma da ƙarfi (wataƙila a jannai ne ko tumbi ko ƙaramin hanji). 

Aman jini, musamman mai yawa zai iya jefa mutum cikin yanayi na ƙarancin isasshen jinin da ya ke zagayawa ga ƙwayoyin halittu (wato SHOCK).

Abubuwan da ke kawo aman jini:

1. Olsa ko gyambon ciki

2. Tasawar jannai ko tumbi ko sashen ƙaramin hanji

3. Yawan amfani da magugunan ɗauke gajiya da ciwon jiki (NSAIDs)

4. Ƙwarnafi mai tsanani

5. Shan giya a yi tatul

6. Daɗaɗɗen ciwon matsarmama

7. Yagewar bututun abinci 

8. Ciwon daji

Maganin aman jini:

Ya danganta da halin da mutum ya shiga a sanadiyyar aman jinin. Ana yin ƙarin ruwa ko ƙarin jini ko kuma sanya wa mutum iskar oksijin. 

Agajin gaggawa:

A yi gaggawar kai mumtum asibiti, idan aman jinin ya haddasa waɗannan abubuwa:

Juwa

Ruɗewa

Ciwon kai mai tsanani. 

Ku tara a rubutu na gaba. Naku, MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

By ukarofi