
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A ranar Talata, 30 ga watan Yuli, masu zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya su ka fitar da wuraren da za a haɗu wanda za a fara daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
An samu bayanin ne cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun wani lauya mai suna Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) wanda shi ne Antoni Janar na masu shirya zanga-zangar inda a ciki ta ke cewa, saƙo ne zuwa ga Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun.
Takardar, ta zayyano wuraren da za a yi zanga-zangar da kuma nuni ga muhimmancin hakan ga tsadar rayuwa da ake fuskanta a Nijeriya.
Wasu daga cikin wuraren a jihohi daban-daban sun haɗa da;
- Abuja: a filin taro na Eagle’s Square da ke Sakatariya, Abuja
- Legas: Tashar Alausa da ke Sakatariya, Ikeja
- Edo: Daura da Bankin Wema, hanyar Akpakpava, a Binin City
- Bauchi: Daura da ‘School of Agric’, hanyar Tafawa Ɓalewa, Bauchi
- OYO: Gidan man Rosewale, hanyar Iwo, Ibadan
- Yobe: Shataletalen Maiduguri, babban Filin wasan Jihar, Damaturu
- Ribas: Shataletalen rainbow da filin wasa na Pantani
- Osun: a Freedom Park, Oshogbo
Ya ce, za su cigaba da bai wa rundunar sauran bayanai yayin da ake cigaba da shirye-shirye.
