Daga AISHA ASAS
Da yawa za su ga darasin namu a matsayin wani sabon salo, ko abin ban mamaki, ko kuma ma su ga rashin dacewar sa, duba da cewa, har zuwa yanzu wani kaso na mutane ba su yarda da ana cin zarafin ‘ya’ya maza ba, musamman ma waɗanda suke da shekaru masu yawa, ciki kuwa har da mazan ‘yan uwansu.
Muna cikin wani lokaci da duniya ta yunƙuro don yaƙin nema wa mata ‘yancinsu, waɗanda suka jima a halin tauyewa da cin zarafi a sassa daban-daban na duniya. Tsayin shekaru aka ɗauka da kafa wannan yaƙi na kare haƙƙin mata, wanda har ya shagaltar da duniya, ta kasa kai kallonta ga mazan da suka jima a cikin irin halin da matan suke ciki, da ma waɗanda suka samu kansu a halin a yayin da ake ƙoƙarin na yaƙi da cin zarafin mata.
Na san mai karatu ba zai rasa tambayar ta ya yaƙi da cin zarafin mata zai iya zama silar cin zarafin maza? Amsar kuwa ita ce, duniya ta ba wa mata dama a wannan ƙarni da muke ciki, ta ririta su, ta mayar da su shagwaɓaɓɓu, da an taɓa su ta miƙe cikin azama ta ci mutuncin wanda ya yi masu.
Wannan gata da mata suka samu ya yi tasiri a wurin wasu ta hanyar amfani da damar wurin gallazawa maza, don sun fi su gata, kuma idan mazan sun kasa haƙuri, suka taɓa su, to fa ido zai koma kan mazan ne, ba wanda zai bi bahasin zancen, abinda kawai ake kallo, an ci zarafin mace.
Bari mu ɗauki misali da finafinan da muke kallo, musamman ma na Turai ko masu aƙida irin tasu, bai zama komai ba nuna mace ta mari namiji, ko ta kai masa duka, ko jifan shi da wani abu da zai illata shi, kuma su kan nuna hakan a matsayin abinda ba a yarda ka mayar ba, idan ma ka mayar, marubucin zai zana ka a matsayin mutumin banza. Abin tambaya shin su mazan jikin ƙarfe ne da su, ba sa jin duka?
Na san wani zai iya cewa, ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba, a wasu lakuta ma akan samu matan da suka fi mazan ƙarfi, kuma ma dai ko sun fi su ƙarfin idan suna dukan su ba sa rama wa ba za su yi masu illa ba?
Harwayau dai a cikin finafinai irin waɗannan ne za a siffanta mai dukan matarsa a matsayin mutum mafi muni a kowane ɓangare (ba na ce yana da damar dukan ba, ko kuma ana samun mutumin ƙwarai da irin wannan hali ba).
Idan mun dawo a tamu alƙaryar, sau da yawa mata da sunan kishi ko wani dalilin su suke illata mazajensu, ta hanyar ji masu rauni ko kisa ma a wasu lokuta, to idan ba cin zarafi ba ne, me za a kira shi?
A wani sa’in za ka tarar mace ta saka mijinta a gaba, ta zage shi ta uwa, ta uba, ko ta rufe masa ƙofar gidan da ya gina da kansa ko yake biyan haya, ko ta yi wa ‘yan uwa ko iyayensa rashin mutunci, ko ta illata dukiyarsa dan kawai ta ba shi haushi. Wata kuwa idan ta riƙa, za ta ci kwalarsa ta hana shi ɗagawa koda ya yi yunƙurin barin gidan don gujewa fushin zuciya, ta dake shi, ko ta zage shi, ko ta buga ma shi makami. Sau da yawa matan da ake kallon an ci zarafin su idan har an bi salsala za a iya samun wani kaso da wannan batu nawa, (ba wai na ce namiji na da hujjar da za ta iya sahale masa dukan matarsa ba, duk kuwa abinda za ta yi masa. Aure ra’ayi ne, idan ta kai ka ƙarshe ko ka yi haƙuri ko kuma ka sake ta).
Bincike ya nuna, akwai kaso mai ɗan dama da ake samu a ƙididdigar mutanen da suka samu kansu a cin zarafi da aka dangantashi da maza.
A ƙasashen Afrika da dama, alƙalluma sun nuna aƙalla ana samun kaso 18 zuwa 30 bisa ɗari na maza da aka ci zarafin su, waɗanda suka haɗa da wuraren ayyuka, iyayensu ko na riƙo, zuwa gidajen aurensu, wato a hannun matansu.
A ɓangaren ƙasashen ƙetare ma, akan samu kaso mai dama na mazan da aka ci zafari ciki har da waɗanda aka yi wa fyaɗe.
Masu iya magana dai sun ce, ‘dokin mai baki ya fi gudu’, don haka shirun da maza ke yi a lokuta da dama ne ke sa ake ganin mata ne kawai ake cin zalin su a zamantakewa tsakaninsu da maza. Amma da za su buɗa baki, su faɗi abinda suka baro ko wanda suke ciki za a tabbatar su ma sun cancanci gangamin nema masu ‘yanci.
Ba na ce a daina abinda ake yi wa mata ba, wannan yaƙin da ake yi masu ya ceto rayuwar mata da yawa daga halin cin zarafi daban-daban. Saidai idan ana tafiya a dinga waiwayar baya, su ma mazan a ɗan leƙa su, don ceto waɗanda suke shan wuya a hannun matan dai da ake ganin masu rauni ne.
