Zan ƙara duba batun shirin zanga-zanga da wasu matasa ke bayyana aniyar gudanarwa daga ƙarshen watan nan ko farkon watan gobe a Nijeriya. Zan fara da wannan kafin shiga batun mafi ƙarancin albashi da ’yan ƙwadago su ka amince da shi. Haƙiƙa daga labarun da mu ke gani akwai waɗanda ke tunanin fitowa kan tituna don zanga-zanga shi ne zai kawo sauƙin rayuwa inda wasu da kuma da su ka haɗa da dattawa da malamai ke jan kunnen yin hakan ba alheri ba ne ga ƙasa. Akasarin masu yayata yin zanga-zanga na yin hakan ne a kafafen yaɗa zumunta fiye da yadda za a ce za su iya kiran taro na musamman don bayyana muradun da su ke son cimmawa.
Gefen masu kore zanga-zanga na yin hakan a fili da ma amfani da kafafen labaru na zamani da na gargajiya. Kamar yadda mu ka kawo zanga-zangar da a ka gudanar a baya ta rikiɗe zuwa ƙiyayyar ƙabilanci da bambancin addini, to hakan shi ne fargabar masu cewa zanga-zanga a Nijeriya ba daidai ba ne don hatta kan ’yan ƙasar ba a haɗe ya ke ba balle har su taru a dandali daya su yada wani muradi. Ko me ya faru a cikin biyu dai Nijeriya na buƙatar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ko abincin da a ke fatan samu zai iya ciyuwa ne in akwai zaman lafiya. Wannan zanga-zanga da za ta zama ta daga kwalaye a gefen tituna ko wasu sassa da baa bun tada hankali don tsarin mulki bai hana zanga-zangar lumana ba. Idan hakan zai juye daga zanga-zanga ya koma banga-banga wato datse tituna da hana sauran jama’a ratsa tituna don tafiya asibiti ko wajajen gaggawa to hakan ya shiga haƙƙin da ba shi da madogara a tsarin mulkin.
Don haka a ke tambaya shin zanga-zanga za a yi ko banga-banga? Ba wanda zai gano irin abun da zai faru daga ɗaukar lamarin sama-sama ba tare da gano asalin masu shirin zanga-zangar ba. Duk mai hankali ko kishin ƙasa ba zai goyi bayan zaman kasa a cikin yunwa ba amma hakan ba ya na nuna sai an yi banga-banga kafin samun maslaha ba. Ni na lura mutane da dama musamman matasa na sha’awar fito na fito ko masu mara baya ga yanayi na zafin rai wajen bayyana kukan jama’a ga gwamnati. Ita kan ta gwamnatin ta dimokuraɗiyya ce da mutane ke zaɓa ko ta kan hau da samun wa’adin shekara hudu ko takwas.
Tun fara sabuwar dimokraɗiyyar Nijeriya an ga sauya hannun shugabanci daga kudu zuwa arewa sannan daga dan arewa zuwa dan kudu. Kowa ya gwada iya salon da zai iya mai ma’ana ne ko marar ma’ana. Duk yadda mutum ya duba lamarin zai ga mutane ne dai ba aljanu ba a cikin gwamnati. Yaya za mu iya samun saukin rayuwa a tsarin Nijeriya shi ne a ke lalume don ganowa. Musamman kamar akasarin ‘yan arewa sun yi ta gwagwarmaya a siyasance don tsohon shugaba Buhari ya hare karaga da su ke kyautata ko ma yaƙinin hakan shi zai kawo sauƙin rayuwa. Shin saukin ya samu ko bai samu ba mun yi farin ciki da har yanzu Nijeriya na nan kasa guda mai al’ummu daban-daban.
Malaman Islama a Nijeriya sun samu saɓanin fahimta kan halal ne ko haram ne gudanar da zanga-zanga don ƙalubalantar salon mulkin shugabanni.
Wannan ya taso ne biyo bayan shirin wasu matasa na gudanar da gagarumar zanga-zanga don nuna damuwa kan ɗan karen tsadar abinci a ƙasar.
Abun da ya fi tsananta kalaman malaman kan zanga-zangar shi ne furucin wani matashi da ke cewa a ingije malami daga kan mumbari matuƙar ya hana gudanar da zanga-zangar.
Wani limami a Kaduna Malam Sunusi Khalil na daga cikin waɗanda su ka fi fusata kan bijirewa malamai masu ƙin jinin zanga-zanga.
Duk da an samu malaman da su ka ɗau matakin tsaki-tsaki kan zanga-zanga amma wasu na cewa halal ne kai tsaye a irin yanayin Nijeriya yayin da wasu ke cewa haram ne.
Farfesa Mansour Ibrahim Sokoto na daga malamai masu nuna zanga-zanga ba daidai ba ne don ba zai haifar da alheri ba.
Amma shaharerren malamin Islama Dokta Ahmad Gumi ya ce zanga-zanga ne yaren da gwamnati ke ji duk da ya hori matasan da gujewa wuce gona da iri.
A sharhinsa Farfesa Sadik Umar Gombe ya ce jigon dimokraɗiyya ne gudanar da zanga-zangar lumana.
A cibiyar kasuwancin arewa wato Kano sakataren majalisar haɗin kan malamai Dr. Sa’idu Dukawa ya kawo maslahar da ta hada da addu’a da samawa matasa ayyukan yi.
Za a jira zuwa ƙarshen wata don ganin yiwuwar wannan zanga-zanga wacce a tsarin kururuta ta sai dai a kwatanta da zanga-zanagr yaki da zargin zaluncin ’yan sandan SARS zamanin tsohuwar gwamnatin Buhari.
Da ya ke amsa tambaya daga wakliyar Muryar Amurka Sheikh Dokta Ahmad Gumi ya buƙaci matasan Nijeriya da ke shirin gudanar da zanga-zanga su jinkirta hakan don ganin sakamakon saƙon da su ka aika.
Dokta Gumi wanda tun farko ya ce matasan na da ’yancin yin zanga-zanga; ya ƙara da jan kunnen matasan kar su sanya siyasa ko neman wuce gona da iri a zanga-zangar.
Sabuwar matsayar ta Dokta Gumi ta ce gwamnati ta riga ta samu saƙon matasan don haka su jira zuwa kimanin watan Disamba don ganin matakin da za a ɗauka.
Ba wai Sheikh Gumi ya haramta zanga-zanga ƙarƙashin dimokraɗiyya ba ne amma ya na da hangen gwamnati ta gano ƙorafin matasan da halin matsi da ƙasa ke ciki.
Mai da’awar zama Madugun shirya zanga-zangar yaƙi da yunwa da a ke shirin gudanarwa a ƙarshen watan nan a Nijeriya Komred Murtala Garba ya ce sun janye daga shiga zanga-zangar.
Garba a taron manema labaru a Abuja ya ce sun gano akwai lauje cikin naɗi don akwai wani hamshaƙin mai kuɗi a kuɗi da ya ke son amfani da su don shirya zanga-zangar a iya wasu biranen arewa da su ka haɗa da Abuja, Kaduna da Jos.
Komred Garba ya ce an ba su maƙudan kuɗi don cimma wannan manufa amma su ka ga ba riba don haka sun janye daga batun zanga-zangar.
A nan Garba ya ce su na kira ga gwamnati ta dawo da tallafin muhimman abubuwa da ta cire don kawo sauƙi ga jama’ar ƙasa.
Garba ya ce ko da ba za su iya karya lagon zanga-zangar ba amma sun janye kuma su na buƙatar gwamnati ta dau mataki kan masu nacin sai sun fito zanga-zangar.
Mai ba wa shugaban Nijeriya shawara a fuskar yaɗa labaru Bayo Onanuga ya zargi magoya bayan dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Leba Peter Obi da shirin zanga-zangar da a ke ta yayatawa.
Duk masu bin kafafen labaru musamman na yanar gizo na ganin bayanai kan shirin zanga-zangar yaƙi da yunwa a ƙarshen watan nan.
Onanuga kai tsaye ya zargi magoya bayan Obi da zama masu kulle-kullen zanga-zanga don neman kifar da gwamnatin Tinubu.
Onanuga da ma ya saba aikin kare shugaba Tinubu ta irin wannan yanayi amma dai bai fito ya ba da shaidar zargin ba.
Akwai matasan yanar gizo da ba lalle magoya bayan Obi ba ne da ke yayata shirin zanga-zanga da nuna akwai ƙuncin rayuwa a ƙasa.
Malaman Islama na kiran gujewa zanga-zangar don kar ta rikiɗe ta koma ta ‘yan sara-suka ko ɓarayi da ka iya wawashe kayan jama’a.
A na cikin wannan musayar kalamai sai Gamaiyar kungiyar kwadagon Nijeriya ta ce tayin Naira 70,000 da shugaba Tinubu ya yi a matsayin mafi ƙarancin albashi da babu ne gara ba daɗi.
Shugabannin ƙwadagon sun bayyana matsayar gabanin gabatar da tayin ga majalisun ƙwadagon don gamsar da su amincewa da hakan ya fi a’ala.
Wannan dai na nuna a karo na farko tun neman mafi ƙarancin albashi mafi yawa a Nijeriya Naira 615,00 ya sauko Naira 477,000, shugabannin ƙwadagon sun maida wuƙa kube ta hanyar yin na’am da tayin da gwamnati ta yi.
Bayan kammala ganawa babban sakataren ƙungiyar ƙwadago ta TUC Komred Nuhu Toro ya ce sun amshi tayin da gabatar da hakan gaban majalisun su “mun kai majalisar kolinmu, tayin da shugaban kasa ya bayar sun kuma lamunta da shi da fatan Allah ya sa albarka…ai Naira 70,000 din nan da babu ne gara ba daɗi.
Tuni ma’aikata na sassa daban-daban su ka fara maida martani da mafi sauƙi shi ne na nuna ba abun da su ka iya don jagorori sun amince.
Malamin makaranta Muhammad Bello Nawaila ya ce ba wani tasiri da mafi ƙarancin albashin zai yi in an duba ɗan karen tsadar rayuwa.
Ita ma ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyin arewa CNG da ke marawa gwagwarmayar ma’aikatan baya ta ce matuƙar shugaba Tinubu bai yi garambawul ga lamuran walwalar ma’aikata da matasa ba, za a iya fuskantar ƙalubale “mu na gujewa guguwar juyin juya hali a Nijeriya matukar gwamnati ba ta farka ta ɗau matakan gaskiya na zahiri ba.”
Alamu na nuna batun neman ƙarin mafi ƙarancin albashi zai dakata zuwa wani lokaci don ’yan ƙwadago sun yada gora sai komawa kan batun tsadar rayuwa.
Kammalawa;
Duk abun da ’yan ƙasa za su yi su riƙa duba maslahar da hakan zai haifawa ƙasa kafin gudanar da shi. Harkokin yau da kullum ko cigaban ƙasa ba zai tabbata ba ba tare da natsuwa, ilimi da hangen nesa ba. Duk hukuncin da mutum zai yanke ya kaucewa yin hakan a lokacin da ya ke cikin hushi.
