
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya yaba wa ƴan zanga-zangar da ke ƙalubalantar matsin rayuwa da ake fama da shi a Nijeriya.
Yayin da ya ke jinjina wa ƙoƙarin nasu, Atiku ya kuma yi alla-wadai da ɓata-gari da su ka sauya zanga-zangar a wasu jihohin zuwa tarzoma.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro kan irin yadda su ke gudanar da ayyukansu da kuma kaurace wa cin mutuncin ƴan jarida ko kuma hantararsu.
Har’ilayau, Atiku ya yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sassauto daga tsarinsa tare da sauron koken al’ummar ƙasa domin a samu daidaito game al’amuran da ke damun su.
