
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojoji ba su yi sata a ɗakin ajiya na Barakat ba, sai dai sun ƙwato ababan da ɓata-gari su ka sace da sunan zanga-zanga.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya faɗi hakan la’akari da wani bidiyo da ke nuna cewa jami’an rundunar sun shiga sahun masu satar kayayyaki a ɗakin ajiyar a ranar Alhamis.
Ya ce, akwai kuskuren fahimta game da fahimtar da jama’a su ka yi wa bidiyon, ya na mai cewa jami’an na runduna ta uku, an kira su ne don su kawo ɗauki kan satar da ake yi a wajen.
Bayan da jami’an su ka ƙwato wasu daga cikin ababan da aka sata a kan hanyarsu da dawowa, sai aka kira su zuwa Fadar gwamnatin jihar.
Daraktan ya ƙara da cewa, hukumar ɗakin ajiyar Barakat ɗin sun yaba wa ƙoƙarin jami’an tare da jinjina mu su a wani saƙo da babban manajan wajen ya aika zuwa gare su.
Kazalika, ya kuma yaba wa jami’an kan ƙoƙarinsu wajen ganin an kiyaye doka da oda gami da dakatar da ayyukan ɓata-gari.
