Daga MAHDI M. MUHAMMAD
’Yan bindiga sun mamaye yankuna 102 a Jihar Zamfara, inda suka daƙile ayyukan noma a gonaki da dama.
Jihar Zamfara da aka santa da noma, sana’ar noma ta durƙushe a jihar sakamakon yawaitar ayyukan ‘yan fashin daji da suka fara a shekarar 2009 zuwa 2012.
Wannan tashin hankalin ya sa noma ya kusa gagara, musamman a yankunan karkara.
Mazauna jihar, waɗanda sama da kashi 90 bisa 100 sun dogara ne kan noma, an tilasta musu yin watsi da gonakinsu.
Fiye da kashi 70 na mazauna karkara sun yi gudun hijira zuwa birane domin gujewa hare-haren ‘yan bindiga.
Waɗanda suka rage sau da yawa ɓarayin suna tilasta musu biyan haraji. Sama da ƙauyuka 200 ne yanzu babu kowa a cikin su saboda yawan hare-hare da buƙatu daga waɗannan masu laifi.
Mallam Garba Musa, wani babban manomi a yankin Dada da ke ƙaramar hukumar Zurmi, ya bayyana cewa gonaki da dama sun zama wuraren kiwo ga dabbobin ‘yan fashin dajin.
Bincike ya nuna cewa ƙauyuka da yawa a cikin ƙananan hukumomi da dama babu komai.
A ƙaramar hukumar Zurmi, an yi watsi da ƙauyuka kamar Gidan Labbo, Tsakauna, Dogon-hako, da dai sauransu.
A ƙaramar hukumar Tsafe, yankunan kamar Munhaye, Dutsin Kura, Kekawa na ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga.
ƙaramar hukumar Maru ta ga ƙauyuka kamar su Madada, Bingi, da Kabaro sun zama kowa. ƙauyukan ƙaramar hukumar Anka da suka haɗa da Rafin Danya da Barayar Zaki suma abin ya shafa.
ƙananan Hukumomin Maradun, Talata-Mafara, da Gusau suna da ƙauyuka da yawa da wannan abu ya shafa.
Alhaji Abubakar Nakwada sakataren gwamnatin jihar Zamfara ya bayyana cewa gwamna Dauda Lawal ya ƙuduri aniyar ganin manoma sun koma gonakinsu a wannan kakar.
Gwamnatin jihar ta haɗa kai da jami’an tsaro domin magance barazanar ‘yan fashin.
Nakwada ya jaddada cewa gwamnati ba za ta yi sulhu da ‘yan bindigar ba, amma za ta tunkare su domin dawo da tsaro a jihar.
