Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar sojin Nijeriya ta sallami wasu sojoji shida daga aikinta bisa zarginsu da tserewa daga wani harin da ƙungiyar Boko Haram ta kai a garin Damboa na jihar Borno.
Sojojin da ke aiki da rundunar Operation Lafiya Dole, an ce sun janye daga fagen daga ne bayan harsasan su sun ƙare a yaƙin da su ke yi da ‘yan ta’adda.
Sojojin da aka kora sune: PTE OLANIYI EMMANUEL (19NA/78/0690); PTE MASA’UDU ADAMU (20NA/79/3745); PTE ABDUL AZEE SALEH (22NA/82/5192); PTE MOHAMMED MOHAMMED (22NA/82/1721); PTE ADAH TOYE (22NA/82/1191); PTE HASSAN ABUBAKAR (22NA/82/1909).
Wata majiyar sojin ta bayyana hukuncin a matsayin rashin adalci, inda ta bayyana cewa sojojin sun gudu ne bayan sun gama da harsashin su.
Majiyar ta ɗora alhakin rashin isassun makamai da alburusai ne ya jawo gazawar sojojin wajen yaƙar maharan yadda ya kamata.
Majiyar ta kuma danganta mutuwar sojoji sama da 10 a yayin harin da rashin wutar lantarki da kuma rashin isassun kayan aiki.
“’Yan Boko Haram sun yi nasarar kutsawa wurinmu a cikin watan kuma suka haddasa mutuwar wasu sojoji da yin garkuwa da wasu. Don haka wasu daga cikin abokan aikinmu sun gudu a lokacin yaƙin, kuma duk an tuhume su da korarsu saboda rashin mayar da martani,” inji shi.
Sojojin Nijeriya da ke fagen fama sukan koka kan yadda ake ba su ƙarancin kayan aiki domin tunkarar mayaƙan Boko Haram.
Ya kuma ɗora alhakin mutuwar waɗanda aka kashe a kan rashin isassun wutar lantarki da kuma rashin isassun kayan aiki don yaƙar ’yan tada kayar bayan.
