Hukumar ’yan sanda ta sanar da fara horar da sabbin ƙananan jami’ai

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD 

A ƙarshe, Hukumar ‘Yan Sanda ta sanar da fara horar da sabbin jami’an ‘yan sanda da aka ɗauka aiki.

Lamarin dai na zuwa ne biyo bayan wani zazzafar rikicin da ya ɓarke tsakanin hukumar da rundunar ‘yan sandan Nijeriya dangane da jerin sunayen jami’an da suka samu gurbi.

Taƙaddamar ta taso tsakanin hukumar PSC da rundunar NPF bayan da aka fitar da jerin sunayen mutane 10,000 da suka yi nasarar samun aikin ɗan sanda da kwararrun jami’an ‘yan sandan Nijeriya a ranar 4 ga watan Yuni.

Rundunar ‘yan sandan dai ta yi watsi da jerin sunayen, inda ta yi zargin cewa aikin ɗaukar ma’aikatan an yi shi ne cikin cin hanci da rashawa.

Sai dai hukumar ta sha alwashin ba za ta soke jerin sunayen ba, lamarin da ya sa ministan harkokin ‘yan sanda, Ibrahim Gaidam da sauran masu ruwa da tsaki suka shiga cikin lamarin.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, PSC ta ce hukumar ɗaukar ma’aikata ta ‘yan sanda ta amince da ranar 10 ga watan Agusta, 2024 domin fara horar da waɗanda suka yi nasara a aikin ɗaukar ma’aikata na shekarar 2022.

Ya ce, “Ana sa ran sabbin jami’an za su tabbatar da matsayinsu ta hanyar shiga sashin intanet na – https://apply.Policerecruitment.goɓ.ng don tabbatar da ƙarin cikakkun bayanai game da horon.

“Duk da haka, sabbin jami’an za su dawo horon watanni biyu bayan na takwarorinsu na Big Duty suka kammala. Za a sanar da bayanai game da kwanan wata da wuraren da za a horar da su na musamman a lokacin da ya dace.

“Hukumar ‘yan sanda na fatan yaba wa masu neman aikin saboda haƙuri da fahimtarsu yayin da aka yi ƙoƙarin tabbatar da cewa aikin ya hada da kuma karɓuwa gaba daya.

“Hukumar ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da tabbatar da cewa ɗaukar aikin ‘yan sandan Nijeriya ya dogara ne da cancanta da mutunta ƙa’idojin Tarayya.

“Ya kuma umarci sabbin jami’an da suka yi nasara da su ga sabon matsayinsu a matsayin kira zuwa ga al’ummar Nijeriya tare da jaddada cewa hukumar za ta sanya ido kan shirye-shiryensu na horar da su domin tabbatar da cewa sun fito a shirye domin haɗaƙkarfi da ƙarfe wajen yaai da ƙalubalen tsaro da ƙasarmu ke fuskanta.”

By ukarofi