Bagudu ya bayyana abinda Tinubu ya ke yi yayin da ake zanga-zanga

Spread the love

Ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu yana bibiyar zanga-zangar da ke wakana a faɗin ƙasar yayin da shiga rana ta uku.

‘Yan Nijeriya da dama ne ke nuna fushin su sabida tsada da kuma ƙuncin rayuwa da ake fama dashi wanda ya fara ne sanadiyar cire tallafin man fetur da shugaban yayi shekara ɗaya da ta wuce.

Bagudu ya ce, Shugaba Tinubu na bibiyar al’amarin kuma zai ɗauki mataki na gaggawa domin ganin a samar da sauƙi ga ‘yan Nijeriya.

Zanga-zangar ta tafi lafiya a jihohi da dama a ranar farko, kafin kuma ta rikiɗe ta koma fitina, wanda ya tilasta wasu jihohi sanya dokar hana zirga-zirga.

By ukarofi