Kayan abinci za su sauko – Kwastom ga masu zanga-zanga

Spread the love

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da cewa farashin abinci zai ragu sosai nan ba da jimawa ba.

Shugaban hukumar Kwastam na Najeriya, Bashir Adeniyi, ne ya bayyana hakan a hedkwatar tsaro, Abuja, ranar Talata, 6 ga watan Agusta, 2024.

Adeniyi na daga cikin shugabannin hukumomi da suka halarci taron sirri na tsare-tsare da shugaban hafsan soji, Janar Christopher Musa, ya kira.
Za a iya tunawa cewa, dubban ‘yan Najeriya sun shiga zanga-zanga a faɗin ƙasa ranar 1 ga watan Agusta, inda suka gabatar da buƙatu daban-daban, ciki har da matsalar tsadar abinci da hauhawar farashi.

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron tsare-tsare, shugaban hukumar kwastam ya ce wasu daga cikin abincin da ake shigo da su a ƙasar, za a cire haraji a kansu domin rage farashin su.

Ya ce, “Zanga-zangar ta dogara ne kan abubuwa da dama, ɗaya daga cikinsu shi ne yunwa. Mun gano cewa ana shigo da abinci mai yawa da ake ci a Najeriya.

“Shigo da abinci yana ɗaukar lokaci. Don haka ɗaya daga cikin abubuwan da shugaban ƙasa ya yi don rage tasirin tsadar shigo da abinci shi ne dakatar da haraji da sauran kuɗi a kan abincin da ake shigo da shi na wani lokaci.
Mun aminta cewa idan aka aiwatar da wannan, zai taimaka wajen rage farashin abinci a kasuwa.

By ukarofi