Olympics: Dalilan da suka sanya ƴar Nijeriya karawa da keken aro – Ministan Wasanni

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ministan wasanni, John Enoh ya yi bayanin dalilan da su ka sanya ƴar wasan gudu a ɓangaren keke, Ese Ukpeseraye ke amfani da keken aro wajen karawa da takwarorinta a cigaba da gasar Olympics da ke gudana a Farisa, babban birnin ƙasar Faransa.

Ƴar wasan wacce ta wallafa a shafinta na X cewa, la’akari da sanar da ita da aka yi batun lokacin karawar cikin ƙurarren lokaci wanda hakan ka iya sa ta rasa damar shiga sahun masu fafatawar, ya sanya ta karɓar aron na takwararta na ƙasar Jamus.

A lokacin da ya ke magana game da batun da ƴar wasan ta wallafa, Ministan ya ce, an sauya tsarin tseren keken ne inda aka sanya Nijeriya bayan cire wata ƙungiya wanda akwai buƙatar amfani da keke wanda idan aka biya kuɗinsa zai ɗauki tsawon watanni kafin a karɓe shi.

Enoh ya kuma nanata cewa ƙungiyar ɓangaren Nijeriya ta hannun ƙungiyar ƴar wasan da ke Nahiyar Turai da wani kamfanin mallakar Jamus su ka samar mata da keken domin shiga gasar.

Kazalika, ya tabbatar da ƙoƙarin ƙasar na mu’amalantar baki ɗaya ƴan wasan guje-guje da tsalle-tsalle cikin mutuntawa, don haka Ese za ta samu keke domin fafatawa a gasar.

By Babaji