Ambaliya ta yi awon gaba da titin Kano zuwa Maiduguri

Spread the love

Wani mamakon ruwan sama da aka yi, yayi awom gaba da titin Maiduguri zuwa Kano tsakanin ƙauyen Malori da Guskuri a ƙaramar hukumar Katagum a Jihar Bauchi.

Ruwan ya haddasa dole masu bin hanyar neman mafita dalilin wannan hanyar ba zata biyu ba yanzu.

A wata ziyarar gani da ido da gwamnan ya kai wurin, gwamnan ya jaddada irin muhimmancin da titin yake dashi musamman in an yi la’akari da shine ya haɗa Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas a Nijeriya.

Yayin ganawa da manema labarai, gwamnan yayi kira da gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar gyara wannan titin domin mutane su cigaba da harkokin su bisa shi.

Jihar Bauchi ta fuskanci tsananin ambaliyar ruwa a wannan shekarar wanda yayi sanadiyar asarar dukiyoyi da dama.

By ukarofi