HOTUNA: Sarkin Kano Sanusi ya ziyarci cibiyar sadarwa da masu zanga-zanga suka ɓata a Kano

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi ziyarar gani da ido cibiyar sadarwa ta zamani da Gwamnatin Tarayya ta gina a Kano ƙarƙashin Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), wacce wasu masu zanga-zanga suka ɓarnata ta.

A ranar 7 ga Agusta, 2024, ne Mai Martaba Sarkin ya kai ziyara cibiyar ta ‘Nigerian Communication Commission Digital Indstrial Park’, wacce Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gina da nufin bunƙasa harkokin sadarwa ta zamani, wacce aka tsara dubunnan matasa a Kano da maƙotan jihohi za su samu aikin yi a ƙarƙashin shirin.

Sarki Sanusi ya jajenta tare da jan hankalin al’ummar Kano da su daina yin irin wannan ɓarna, domin a kan talakawa ta ke ƙarewa.

A ƙarshe, ya yi addu’a tare da neman zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Kano.

By Babaji