Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Spread the love

West Ham na neman ɗaukar ɗan wasan bayan Chelsea da Ingila mai shekara 26, Treɓoh Chalobah, da kuma ɗan wasan bayan Jamus mai shekara 35, Mats Hummels, wanda kwangilarsa da Borussia Dortmund ta ƙare a bana.

Crystal Palace na zawarcin ɗan wasan bayan Chelsea Chalobah, ta na kuma bibiyar ɗan wasan bayan Faransa mai shekara 24, wanda ke leda a Wolfsburg, Maxence Lacroix.

Har yanzu Liverpool na da sha’awar ɗaukar ɗan wasan gaban Jamus da Hoffenheim, Maximilian Beier, amma ɗan wasan mai shekara 21 ya fi son komawa Borussia Dortmund.

Ɗan wasan bayan Aston ɓilla mai shekara 31, Lucas Digne ya ƙi amincewa da tayin komawa taka leda a Galatasaray. Ana sa ran ɗan wasan Faransan ya ci gaba da zama a ɓilla.

Valencia ta dakatar da tattaunawar sayar da ɗan wasan tsakiyar Sifaniya mai shekara 21 Javi Guerra ga Atletico Madrid.

West Ham na zawarcin ɗan wasan bayan Ingila mai shekara 33, Kieran Trippier, wanda kwangilarsa da Newcastle ke ƙarewa kuma babu wata alamar tsawaita ta.

Da alama Manchester United za ta gabatarwa ɗan wasan tsakiyar Burnley da Norway mai shekara 26, Sander Berge tayin kwangilar yuro 100,000 kowanne mako domin ɗaukar shi zuwa Old Trafford.

Chelsea ta amince, za ta biya Atlentico Madrid yuro miliyan 35m domin ɗaukar ɗan wasan gaban Sifaniya mai shekara 20, Samu Omorodion. Wata majiya ta ce ɗan wasan ya shirya zuwa a gwada lafiyar sa gabanin ƙulla yarjejeniyar.

Ana sa ran ɗan wasan tsakiyar Real Sociedad, Martin Zubimendi zai amince da sauya sheƙa zuwa Liɓerpool amma har yanzu ɗan wasan mai shekara 25 bai ƙulla yarjejeniya ba kawo yanzu.

an wasan gaban Albania mai taka leda a Chelsea, Armando Broja zai gana da kocinsa Enzo Maresca domin cimma matsaya a game da makomarsa. Eɓerton da Wolɓes na daga cikin masu bibiyar ɗan wasn mai shekara 22.

By ukarofi