Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Matatar Sukarin Dangote ta bayar da rahoton asarar Naira Biliyan 104.6 a tsakiyar shekarar 2024, wani gagarumin raguwar kashi 110 da aka samu a shekarar 2023.
Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, kamfanin ya fitar da kashi na biyu na kuɗaɗen shiga na shekarar 2024 na Naira biliyan 172.9, wanda ya ba da gudunmawar kuɗaɗen shiga na rabin shekara na Naira biliyan 295.6.
Wannan adadi na kuɗaɗen shiga ya nuna kƙruwar kashi 72 cikin 100 duk shekara daga Naira biliyan 100.6 da aka samu a kwata na biyu na 2023.
Sai dai kuma, ƙarin kashi 140 cikin 100 na farashin sayarwar kamfanin ya haifar da raguwar ribar da aka samu da kashi 71 cikin 100 a duk shekara, inda ya ragu zuwa Naira biliyan 9.4 daga Naira biliyan 32.4 a kwata na biyu na shekarar 2023.
Haka kuma ribar aiki ta ragu da kashi 83 cikin 100 duk shekara, inda ta ragu zuwa Naira biliyan 5.03 daga Naira biliyan 29.3 a shekarar da ta gabata.
A farkon rabin shekarar 2024, sukarin Dangote ya yi asara mai yawa da ya kai Naira biliyan 193.7, wanda ya ƙaru da kashi 133 cikin 100 daga asarar Naira biliyan 83.1 a farkon rabin shekarar 2023.
Wannan ya fari ne a sanadiyyar hauhawar farashin kaya, wanda ya haura kashi 158 cikin 100 a duk shekara zuwa Naira biliyan 234.2 daga Naira biliyan 90.7, ya yi tasiri sosai ga harkokin kuɗin kamfanin.
