Daga MADHI M. MUHAMMAD
’Yan Majalisar Wakilai har yanzu ba su aiwatar da ƙudurin da suka sanya wa hannun na zaftare albashin su da kashi 50 cikin ɗari na watanni shida masu zuwa ba.
’Yan majalisar tarayya sun yanke wannan ƙudiri ne a ranar 18 ga watan Yuli kuma ana sa ran za a yi la’akari da tara zaftare albashinsu na watan Yuli, amma mai magana da yawun majalisar, Rotimi Akin, ya ɗora alhakin jinkirin aiwatar da aikin a kan tsarin gudanarwa.
“Majalisar wakilai ta ci gaba da jajircewa kan ƙudurin da aka zartar a ranar 18 ga watan Yuli, wanda ya buƙaci a rage kashi 50 cikin 100 na albashin mambobi daga watan Yuli zuwa Disamba 2024.
“Mun amince kuma mun yi nadamar cewa wannan ƙudiri bai fara aiki ba kamar yadda aka tsara a watan Yuli.”
’Yan majalisar sun yi wannan alƙawari ne a lokacin da suke tattaunawa kan wani ƙudiri, na neman daƙile zanga-zangar yunwa a faɗin ƙasar, wadda aka fara a ranar 1 ga watan Agusta.
