Za mu canja tsarin tafiyarmu ta siyasa a Jihar Katsina – Musa Bature

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wani matashi kuma jigo a tafiyar siyasar jam’iyyar NNPP a Jihar Katsina, Alhaji Musa Bature Bakori dake cikin Jihar Katsina, ya jagoranci gudanar da taron neman haɗin kawunan tsofaffin shuwagabannin Jam’iyyar ta NNPP da sauran ‘ya’yanta na shiyyar Funtuwa da kewayenta gaba ɗaya.

Taron wanda ya samu halartar dukkan tsofaffin shuwagabannin jam’iyyar ta NNPP a shiyyar Funtuwa ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Musa Bature Bakori a ranar Asabar ɗin makon jiya.

Alhaji Musa Bature Bakori ya ce sun yi gangamin kiran wannan taro ne domin tattaunawa a bisa kan rashin ingantaccen shugabanci tare da jagoranci mai kyau a jam’yyar NNPP a matakin shugabancinta na ƙasa da ma jihohi baki ɗaya.

Ya ce domin idan ka kalli al’amarin babu kyakkyawan tsari a tafiyar baki ɗaya, a cewarsa hakan ta sanya suka yi gangamin kiran wannan taro domin tattaunawa tare da nemo hanyoyin mafita  dangane da wannan al’amari, inda jagoran taron Musa Bature bakori yaba tsofaffin shuwagabannin jam’iyyar ta NNPP na shiyyar Funtuwa damar suma su kawo nasu shawarwarin  inda tsofaffin shuwagabannin suka ci gaba da bayar da shawarwarin ɗaya bayan ɗaya tare da gabatar da ƙorafe-ƙorafensu na rashin kyakkyawan tsari tare da jagoranci mai kyau na jam’yyar ta NNPP a matakin jihohi dama tarayyar Nijeriya baki ɗaya.

Jagoran gudanar da taron Musa Bature ya ci gaba da cewa hakan ta sanya suka ga ya kamata su tsayar da shawarar cewar sun yanke hukuncin cewa za su juya akalar tafiyarsu ta siyasa daga yanzu zuwa ‘yan lokuta kaɗan masu zuwa.

Ya ce domin idan suka ci gaba da bin wannan tafiya tafiyar ba za ta haifar masu da ‘ya’ya masu idanuwa ba, inji shi.

 Kazalika ya yi kira ga matasan Bakori da ma na jihar Katsina baki ɗaya da su ƙara ƙoƙari wajen neman ilimin zamani da ma na Islamiyya domin kauce wa shiga halin kaka-ni-kayi wajen gudanar da harkokin rayuwarsu ta duniya da ma lahira baki ɗaya.  

By ukarofi