Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kammala ayyukan da ta fara a jihar Katsina.
Kwamishinan filayen da safayo Faisal Umar Kaita ya faɗa haka da yake gabatar da takardar koke a madadin gwamnatin jihar a ga mataimakin na musamman akan muzaɓu Khadijah Kareem Omotayo a wajan zauren taron na masu ruwa da tsaki a jihar.
Ya faɗa wasu ayyukan da yace masu mahimmanci da suka haɗa da aikin hanyar da ta tashi daga Katsina zuwa Kano, da layin dogo sai faɗaɗa filin jirgin sama.
Kwamishinan ya bayyana cewa wannan hanya tun lokacin Marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua aka fara shi amma abin takaici har yanzu ba’a kammala.
“Iyakan inda aka kammala shina daga Kano zuwa ina yayi iyaka da Katsina.
Haka kuma ya tabo maganan aikin gina layin dogo da zai taso daga Kano zuwa Katsina ya nufin maraɗi da shima ko diyya baa biya ba ga wadanda aka karɓi filayen su.
Haka Bashi Usman Ruwan Godiya da ya wakilci kungiyoyi yin kare hakkin bil’adama ya kokari ne akan irin yadda shugaban kasa Tunubu ya kewa harkan tsaro a jihar ɗaukan sa kaunar kashi.
Ruwan Godiya wanda yana bayani. Yan na zuba hawaye yace a kullum kashe mutane ake wasu da yawa har yanzu suna hannun yan bindiga,mata kuma dayawa anci zarafin da duban yan gudun hijira.
Sauran waɗanda suka yi magana sun tsokaci akan rashin kammala .anyan madatsun ruwa irin su Sake Dam Abdallawa Dam tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta kammala su da gina wasu a kowace ƙaramar hukuma 34 da ke jihar.
A cewarsu zai taimaka wajen noman rani a jihar tunda dama jihar kasan noma ne da kawar da yunwa sannan ya magance matsalar yunwa da ya cinno kai a ƙasan.
Akwai ƙungiyoyin addinin Musulunci da wakilan sarakunan Katsina da Daura da sauran ƙungiyoyi duka sun gabar da tasu ƙorafe ƙorafe duka akan rashin kammala ayyukan da gwamnatin tarayya ta fara bata ida su ba.
Da take jawabi ban ta karɓi takardar koken mataimakin na musamman akan mazaunan tayi alƙawarin gabatarwa shugaban ƙasa da waɗannan koke.
Ta kuma tabbatar wa gwamnatin jihar cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai yi wani abu akai sai dai su kara hakuri da baiwa gwamnatin sa goyon baya wajan kokarin sa na shawo kan matsalolin da suka adabi ƙasan.
Ta ce jihohi na 9 kenan ta ziyartan kuma za ta ziyarci sauran jihohi da ke faɗin ƙasar.
Da yake rufe taron muƙaddashin gwamnan jihar Faruk Lawal Joɓe ya yaba wa gwamnatin tarayya da ta yi tunanin waiwayo aikin da aka fara a jihar amma saboda wasu dalilai akai watsar da aikin.
