Ɗiyar Gwamnan Nasarawa ta buƙaci a riƙa damawa da mata a harkokin shugabanci

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ɗiyar Gwamnan Jihar Nasarawa, Hussaina Abdullahi Sule ta buƙaci a riƙa bai wa mata damar shugabancin jihar da ƙasa baki ɗaya suma don ba su damar bai da nasu gagaruman gudumawa ga ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Hussaina Abdullhi Sule ta yi kiran ne na musamman a wajen wani babban taron bita na mata na yini 1 wadda aka gudanar a babban ɗakin taro na babbar Jami’ar Gwamnatin Jihar (NSUK) dake birnin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar.

Taron bitar na musamman na kwana guda mai taken: Gano mace dake cikin ki wato “Discoɓery Women In You, wadda ofishin daraktan cibiyar bunƙasar jinsi na fannin ɗalibai na ƙasa baki ɗaya tare da haɗin gwiwar gidauniyar Barade suka shirya suka kuma gudanar yana da manufar jawo mata waje guda ne don samun hadin kansu sa’anan su san damarmakin su da hakokin su da baiwa na musamman da Allah ya yi musu da sauransu.

Da take jawabi a waje n taron matar gwamnan jihar wace ‘yar cikin gwamnan na farkon Hussaina Abdullahi Sule ta bayyana cewa ya dace matuƙa a ci gaba da jaddada muhimmancin damawa da mata a harkokin gwamnati a kuma duka matakan jagoranci shi ya sa taka ya dace ta sa nata baki a koyaushe don mara wa ƙudirin baya inda ta yi kira na musamman ga shugabannin ƙasar nan a duka matakai su riƙa yin la’akari da hakan.

A cewar  Hussaina Abdullahi Sule lokaci ya riga ya wuce da za a riƙa kallon mata a matsayin abu mara muhimmancin maimakon haka a riƙa girmama su tare da tabbatar ana ba su dama kamar yadda ake bai wa takwarorin su maza a duka fannonin rayuwa.

Ta ce ba tana nufin mata suna gaza da maza ba ne amma suna kira ne a riƙa masu dama suma yadda ya dace don suma su riƙa bai da nasu gudunmawa da sauran su kasancewar a cewar ta a duk lokaci da aka ilmintar da ‘ya mace an ilmirtan da al’umma baki ɗaya ne da sauransu.

Ta kuma yi amfani da damar inda ta yaba wa mata a jihar dama ƙasa baki ɗaya dangane da ƙoƙari da suka yi a yanzu wajen neman ilimin addini dama zamani inda ta buƙace su su cigaba da hakan su kuma tabbatar suna bayyana ire-iren kyawawan baiwa da Allah yayi musu don a rika jawosu cikin harkokin shugabancin a ƙasa baki ɗaya.

Daga nan sai ta yaba wa waɗanda suka haɗa taron inda ta ce tabbas shirin zai ce nesa ba kusa ba wajen ɗaukaka matsayin ‘ya mace cikin al’umma a koyaushe nan gaba.

Sauran manyan baƙi masu jawabi a wajen taron da suka haɗa da shugabar jami’ar ta jihar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da mamba mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta tsakiya a majalisar dokokin jihar, Hon. Hajara ɗanyaro da shugaban cibiyar bai wa ɗalibai tallafi na gwamnatin jihar da dai sauran su duk sun yi kira ga shugabanni da gwamnatoti a duka matakai su tabbatar suna tafiya da mata a harkokin shugabancin don ba su damar bai da nasu gudumawa ga ci baban al’umma.

An gudanar da abubuwa da dama a yayin taron musamman tallafin bunƙasar sana’o’i daban-daban da ‘yar gwamnan ɗin wato Hussaina Abdullahi Sule ta bai wa kimanin sama da ɗalibai 10 na jami’ar don inganta sana’o’in nasu wadda ta bayyana cewa karamcin ta yi ne maimakon ta riƙa kashe maƙudan kuɗaɗe wajen bikin ranar haihuwarta dake zuwa kwanan nan.

By ukarofi