ƙungiyar Hamas ta amince ta halacci tattaunawa kan tsagaita wuta a yaƙin da da take gwabzawa tsakaninta da Isra’ila.
Sai dai Hamas ta buƙaci tattaunawar tsagaita wutar da masu shiga tsakani ke jagoranta ta mayar da hankali kan batutuwan da ta amince da su a baya maimakon fara tattauna sabbi.
Amincewar ƙungiyar ta Hamas domin ci gaba da tattauna batun tsagaita wutar na zuwa ne bayan da Isra’ila ta yi luguden wuta tare da hallaka Falasɗinawa 19 a wasu hare-hare da ta kai ta sama.
ƙasar Amurka ta ce za a ci gaba da tattaunawa ranar Alhamis mai zuwa kamar yadda aka tsara kuma ana sa ran cimma matsaya domin tsagaita wuta.
Wata kafar internet a Amurka Aɗios, ta rawaito sakataran harkokin wajen ƙasar Anotony Blinken na cewa shirye-shirye sun kammala domin tattaunawa a ƙatar da Masar da Isra’ila.
Gwamnatin Isra’ila ta ce zata tura wakilai domin tattaunawa ita kuwa ƙungiyar Hamas ta buƙaci a mayar da hankali kan batutuwan da ta amince da su tun a baya.
Isra’ila dai ta hallaka Falasɗinawa 19 a wasu hare-hare da ta kai ta sama a yankunan Deir Al-Balah da sansanin Al-Bureij da Al-Maghazi da yankin Rafah.
Rahotanni na tabbatar da cewa wannan yaƙin da aka share watanni 10 ana gwabzawa tsakanin Isra’ila da Haamas ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 40,000 ita kuwa Isra’ila ta ce sojojinta 300 ne suka baƙuncin lahira
