Ukraine ta ce ba za ta ci gaba da riƙe yankin da ta mamaye a Rasha ba, muddin mahukuntan Moscow suka amince da tayin lafiya tsakanin ƙasashen biyu.
Wannan na zuwa ne bayan sojojin Ukraine sun kutsa cikin yankin Kursk mallakin Rasha a Talatar makon jiya, inda suka ƙarɓe iko da wurare da dama a ƙarkashin farmaki mafi girma da wata rundunar soji daga ƙetare ta kai cikin kwaryar Rasha tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.
Tuni sama da mutane 12000 suka arce daga yankin, yayin da shugaban rundunar sojin Ukraine, Oleksandr Syrsky ya ce, dakarun nasa na riƙe da yankin da faɗinsa ya kai murabba’in kilomita 1,000 a Rasha.
Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Ukraine ta ce, ko kaɗan, Kyiɓ ba ta da aniyar mallake wani yanki na Rasha, amma ta ce, abin da sojojin suka yi bai saɓa wa doka ba.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Ukraine ɗin ta ce, da zaran Rasha ta amince da tayin zaman lafiya kaɗai, to babu shakka sojojin za su fice daga wannan yanki da suka mamaye tare da dakatar da farmakin da suke ƙaddamarwa.
A ɓangare guda, Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta ce, ta yi nasarar daƙile sabbin hare-haren da Ukraine ta ƙaddamar a Kursk.
A cikin watan Fabairun 2022 ne Rasha ta fara luguden wuta kan Ukraine, kuma ta yi nasarar mamaye wasu wurare a cikin ƙasar makwabciyarta.
