Daga JOHN D. WADA a Lafiya
A ranar Larabar da ta gabata ne gidauniyar Atoni-janar wanda shine kuma Kwamishinan Shari’a na Gwamnatin Jihar Nasarawa wato Honorabul Shu’aibu Labaran Majagi wanda aka fi sani da Matawalle dake garin Keffi a jihar, ya gabatar wa kimanin ɗaliban Babbar Jami’ar jihar 140 a ci gaba da bukukuwar cikawar Matawallen shekara 1 a matsayin kwamishinan shari’ar a jihar.
Da take jawabi a wajen taron bai wa ɗaliban tallafin shugabar gidauniyar ta Matawalle Hajiya Hafsat Yusuf Sule ta bayyana cewa an kafa gidauniyar ne da nufin samar da tallafi ga marasa galihu baki ɗaya cikin al’umma da tabbatar da zaman lafiya da tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen taimakon al’umma da sauransu.
Hajiya Hafsat Yusuf Sule ta ce ba shakka Honorabu Shu’aibu Labaran Magaji ya ga ya dace ne ya bai wa ɗaliban tallafin kamar yadda ya saba musamman a wannan lokacin mawuyacin hali da ake fuskanta don rage musu wannan ƙalubalen a yayin da suke karatu.
Shugabar gidauniyar ta Matawalle daga nan sai ta yi amfani da damar ta taya Matawalle murnar bikin nasa na cika shekara 1 a kujera a madadin gidauniyar baki ɗaya kana ta kuma buƙaci ɗaliban da suka amfana da karamcin su tabbatar sun yi amfani da tallafin yadda ya dace don inganta rayuwarsu.
Shi ma da yake jawabi kakakin gidauniyar cigaban matasan Arewa Kwamared Ibrahim Mohammed Lawal ya bayyana taƙaitaccen tarihin kwamishinar shari’an Matawalle ne inda ya kuma miƙa godiyarsa na musamman a gare shi dangane da tallafi da yake bai wa ɗalibai da sauran rukunin al’umma daban-daban a jihar dama ƙasa baki ɗaya inda ya buƙace shi ya ci gaba da hakan kana shi ma ya yi kira na musamman ga ɗaliban su ci gaba da marawa Matawallen baya a koyaushe.
Wakilinmu dai ya gano cewa sauran abubuwa da aka gudanar a wajen taron raba tallafin sun haɗa da raba tsabar kuɗi wa ɗaliban da ɗaukar hotuna inda a ƙarshe wasu daga cikin ɗaliban da suka amfana da karamcin da wakilinmu ya zanta da su duk suka bayyana farin cikinsu tare da yi wa Matawalle fatan alheri da sauransu.
