Daga RABIU SANUSI a Kano
An buƙaci jami’an ‘yan sandan da suka samu ƙarin girma da su ƙara jajircewa wajen kamanta gaskiya da riƙon amana yayin gudanar da aikinsu.
Kiran na zuwa ne daga bakin kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano CP Solomon Garba Dogo yayin da yake ɗaura wa jami’an ‘yan sanda kimanin su 181 ƙarin girma a ranar Litinin.
CP Solomon Garba Dogo ya ce kasancewar ƙwarewa kaɗai ba za ta ba jami’i damar zama a matakin gaba ba kaɗai har sai ya yi wani ƙoƙari na ganin ya tsare aikin sa kamar yadda ya kamata.
“Samun ɗan sanda da bayanai masu nagarta da ƙwarewa yake sawa ya samu ƙarin girma a dukkan aikin da yake yi.”
Dogo wanda ake yi wa laƙabi da (Dogon aiki) ya kuma gode wa Babban Sufeton ‘Yn Sanda na ƙasa Mr Kayode Adeolu da saura manyan mataimakansa wajen yin dukkan mai yuwuwa ganin an samu nasara a wannan hukuma.
Kwamishinan ‘Yan Sandan ya kuma yaba da irin ƙoƙarin jami’an bisa jajircewar su wajen kwantar da tarzoma da kare rayukan al’umma da dukiyoyin su, musamman lokacin zanga-zangar da ta gabata.
Da yake jawabi a madadin waɗanda suka samu ƙarin girman ASP Jacob Yadume, ya bada tabbacin za su ci gaba da aiki tuƙuru cikin ƙwarewar horarwar da suka samu kamar yadda dokar aikin ta tanadar.
