Ƙasashen Afrika da dama na sayen makamai a hannun Nijeriya – Matawalle

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce a yanzu ƙasashen Afrika da dama na sayen makamai da harsasai daga kamfanin samar da makamai na rundunar sojan Nijeriya.

Gwamnatin ta ce hakan ya yiwu ne bayan samar da dokar kafa kamfanin samar da makaman na DICON Act 2023, wacce aka yi don bunƙasa ci gaban Nijeriya da samar da tsaro.

aramin ministan tsaro, Bello Matawalle ne yayi bayanin hakan a ma’aikatar tsaro da ke Abuja a ranar Litinin, yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a bikin cikar kamfanin na DICON shekaru 60.

Za a gudanar da taron bikin cikar kamfanin samar da makaman ne shekaru 60 a jihar Kaduna ranar 14 zuwa 15 ga watan Agusta.

“Muna tabbatar muku cewa muna iya ƙera makamai, kamar yadda kuka sani ƙasashen Afrika da dama na zuwa kamfanin DICON domin siyan makamai da alburushi,”  inji Matawalle.

Matawalle ya kuma bayyana ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da tsaro ta hanyar haɗaka da ci gaban fasahar zamani.

By ukarofi