Zargin rashin gaskiya: Alƙalan babbar kotu 27 za su fuskanci hukunci daga Majalisar Alƙalai

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Majalisar Alƙalan Nijeriya NJC, ta shirya tawagar bincike huɗu domin gudanar da binciken wasu alkalai 27 a Nijeriya kan zargin rashin gaskiya yayin gudanar da ayyukansu.

Sanarwar haka ta fito daga ofishin Daraktan labarai na Majalisar, Mista Soji Oye a ranar Juma’a inda ya ce an ware sauran buƙatu 18 da basu da darajar ɗaukar su daga cikin jadawalin binciken.

Majalisar a zamanta na 106 wacce Shugaban Alƙalan Nijeriya, Olukayode Ariwoola ke jagorantar shari’ar, ya yi nazari kan rahoton kwamitin binciken inda ake tuhumar alkalan manyan kotu-kotu na tarayya da na jiha guda 27 da batutuwa 22.

A yayin haka ne Oye ya aika da saƙon shawara ga Alƙali O. M. Olagunju na babbar kotun jihar Oyo kan cewa ya iya bakinsa bayan da alƙalin ya ƙalubalanci hukuncin Shugaban Alƙalan.

Waɗanda ke cikin jadawalin kwamitin binciken sune; Justice Monica B. Dongban-Mensem, shugabar kotun Ɗaukaka ƙara; Justice E. O. Williams Dawodu; B. A. Gorgewell; Yargata Timpar; S. D. Samchi; Aisha B Aliyu; A. A. Aderibigbe; M. L. Shuaibu; H. A. O. Abiru da Abdulazeez Waziri waɗanda dukan su na kotun Ɗaukaka ƙara ne.

Sauran sun haɗa da; Justice John Tsoho, Shugaban Alƙalan babbar kotun tarayya; Z. B. Abubakar; James Kolawole Omotosho; Sunday B. Onu; da Justice Okon E. Abang, waɗanda ƴan babbar kotun tarayya ne baki ɗayan su.

Sai kuma, Justice Kayode Agunloye na babbar kotun tarayya, Babagana Karumi na babbar kotun tarayya ta jihar Borno, Maimuna A. Abubakar ta babbar kotun tarayya da ke jihar Neja.

Bugu da ƙari, Oye ya ce akwai Alkalai biyar da ake sanya ido akan su waɗanda ƙoƙarinsu ya gaza kima, ya na mai cewa za’a sanya su cikin waɗanda NJC za ta yi wa hukunci matuƙar ba su ƙara ƙoƙari ba.

By Babaji