LP, YPP da AAC sun lashe kujerun kansiloli a Bauchi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Jam’iyyun adawa a jihar Bauchi sun lashe da dama daga cikin kujerun kansiloli a zaɓen da aka yi a ranar Asabar.

A jihar, wacce jam’iyyar PDP ke mulki ƙarƙashin jagorancin gwamna Bala Mohammed, aka samu Samira Maikano ta lashe kujerar gundumar Wandi da ke ƙaramar hukumar Dass a jam’iyyar YPP.

Samira ta samu ƙuri’u 1,610 wanda hakan ya ba ta galaba akan abokin hamayyarta na kusa Bashir Abdullahi na jam’iyyar PDP da ya samu ƙuri’u 1,352 yayin da APC ta samu kuri’u 230.

A ƙaramar hukumar Darazo, Yunusa Muhammad na jam’iyyar AAC shi ya lashe zaɓen a gundumar Papa ta Arewa da ƙuri’u 1,156 inda ya doke takwaransa na jam’iyyar PDP mai ƙuri’u 1,053 da na APC mai 290.

Lucy Yusuf ta jam’iyyar LP ita ta lashe zaɓen gundumar Lusa ta ƙaramar hukumar Ɓogoro da ƙuri’u 2,200 wanda hakan ya ba ta nasara akan takwaranta na PDP mai ƙuri’u 2,168 da kuma na APC mai 275.

By Babaji