Daga AHMADU KANKAROFI
Jihar Kano, wadda ita ce cibiyar kasuwanci ta ƙasar Nijeriya, tana da ƙananan hukumomi guda 44, wanda hakan yake nufin tafi kowace jiha yawan adadin ƙananan hukumomi a duk jihohin da ke tarayyar Nijeriya. Jihar Kano har ila yau an raba ta gida uku kamar yadda aka raba kowace a matsayin sanatoriya, waɗanda suka haɗa da Kano ta Tsakiya, Kano ta Arewa da kuma Kano ta Kudu. Rubutunmu zai taƙaita ne a iya Kano ta Tsakiya wadda take da adadin ƙananan hukumomi guda 15 a ƙarƙashin wannan Sanata mai wakiltar mazaɓar ɗan majalisar dattawa mafi girma da yawan al’umma a Nijeriya inda kuma a yanzu Sanata Rufa’i Sani Hanga shine wakilinta a Majalisar Dattijai da ke babban birnin Tarayya, Abuja.
Wasu marasa kishin jiha da yankin Kano ta Tsakiya suna amfani da wani faifan bidiyo da suka tsakuro suna yada cewar wai Sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce shi ma wai yunwa yake ji. Kaico! Ko da ma da gaske ne, maganar da suke yaɗawa, menene laifi don shugaba ya ce yana tare da al’ummarsa a irin mawuyacin halin da suke ciki? Shi fa ba gwamna ba ne, balle a ce ana turo masa ‘grant’ da zai aiwatar da aikin jinƙan al’umma, da kuɗinsa yake mafi yawan ayyukan jinƙan al’umma da yake yi. Kuma har yanzu, kusan watanni takwas (8), gwamnatin tarayya ba ta saki kuɗaɗen gudanar ayyukan mazaɓu na ‘yan majalisa na wannan shekarar ba, balle su yi aikin da yakamata a ce sun yi.
Ga wanda ma bai san wanene Sanata Rufa’i Sani Hanga ba, ko kuma ma wanda ya sani ɗin, to ga ‘yar matashiya ta wanene Sanata Hanga.
An haifi Sanata Rufa’i Hanga a ranar 18 ga wata Agustan shekarar 1954 a unguwar Hanga cikin birnin Kano, a ƙaramar Hukumar Birni. Ya kammala karantunsa a sha’anin lissafin kuɗi kuma yake da ƙwarewar aikin gwamnati ta sama da shekaru 30. Sanata Rufa’i Hanga ya fara harkokin siyasa ne a shekarar 1979. Ya taɓa zama cikakken ɗan jam’iyyar PRP a ƙarƙashin jagorancin Marigayi Malam Aminu Kano. Kuma tun daga wancan lokaci kullum siyasarsa ta ɓangaren ci gaban jama’a yake yi. Sanata Rufa’i Hanga ya taba zama Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya a shekarar 1992. An kuma zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattijai ta Tarayya a shekarar 2003 zuwa 2007. Kuma a lokacin da yake zaman ɗan majalisa a dukkanin majalisun guda biyu, ya riƙe shugabancin kwamitoci a Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai.
Sanata Hanga ya kuma zama mataimakin bulaliyar marasa rinjaye na majalisar a 2023. Kuma a lokacin yana daya daga cikin ‘yan ƙalilan din ‘yan majalisar da mukami ko ƙarfin iko bai rufe musu idanu ba, bai zama irin waɗanda suke amfani da damarsu wajen cusgunawa mutane ba, duk alƙawarin da ya ɗauka zai cika, kuɗin da yake samu ba ya sa shi girman kai, sannan kuma baya amfani da hukumomi wajen kare kansa. Takwarorinsa da suka samu irin wannan damarmakin da suka kurbi giyar mulki kuma ta rude su, sun yi amfani da karfin ikon da suke da shi wajen biyawa kansu bukatunsu, sun yi amfani da mukamansu wajen arzuta kansu, sun mance da irin nauyin al’umma da ke kansu a matsayinsu na wakilan al’umomin da suka jajirce wajen zaɓensu zuwa muƙaman da suke riƙe da su.
Duk lokacin da iska ta kaɗa, tana ɗauko abubuwa da yawa daga nesa, da kuma na kusa, don irin ayyukan da Maigirma Sanata Rufa’i Sani Hanga ya shafi ko’ina da ina a yankin Kano ta tsakiya .
Lokacin da za a gudanar da zaɓuɓɓukan shekara ta 2023, Sanata Rufa’i Sani Hanga bai yi niyyar shiga zaben ba. Amma aka sauya sunan dan takarar bayan ya fita daga jam’iyyar tasu aka mika sunan Sanata Hanga. Amma ya za kai da hukuncin Allah? Da yake shi Allah Ya bawa, sai ga shi ya sake zama Sanata a Majalisar Dattijai ta Tarayya Mai Walkiltar Al’ummar Gundumar Kano ta Tsakiya, a karo na biyu.
Eh, a karo na biyu, domin shi ne Sanatan da ya karya alƙadarin nan da ake cewa wai ba wanda ya taba kuma ba wanda zai taba yin Sanatan Kano ta Tsakiya sau biyu. Shi kuwa Sanata Hanga ya bar wannan tarihin, domin a shekarar 2003, zabe karo na biyu da aka gudanar a Najeriya tun bayan dawowar mulkin dimokaradiyya a shekarar 1999, Sanata Hanga ya lashe wannan zaɓe inda ya kammala aikin a wancan karon a shekarar 2007.
Kuma shi ne shugaban jam’iyyar CPC na ƙasa na farko a Nijeriya daga 2009 zuwa 2011 kafin su haɗe da sauran jam’iyyu.
Ayyukan da Maigirma Sanatan Kano ta Tsakiya Sanata Rufa’i Sani Hanga ya aiwatar ga al’ummar mazaɓarsa da ‘yan mazaɓarsa sun hada da: Ya biyawa daliban BUK 200 kudin makaranta; ya bawa mata jari na dubu 50k, 30k 20k kimanin mata 1130; ya biyawa yara kuɗin jamb mutum sama da 1000; ya rabawa marayu sama da 2000 kayan sakawa; ya bawa mutum sama da dari 500 Schorlaship a Kano polytechnic; ya rabawa makarbartu tukwane da likafani saboda mamata;ya saka an rabawa dalibai littafai. Ya rabawa wasu nakasassu kekunan Guragu? Ya rabawa mutane tallafi daga gwamnatin tarayya ga mutune sama da 7000, mutum 3500 da doriya sun samu Naira dubu 50, ya raba kayan abinci a kowacce karamar hukuma 15 da ke cikin Gundumar Kano ta Tsakiya da yake wakilta inda kowacce karamar hukuma ta rabauta da buhu 450 na abinci kamar su shinfaka, taliya, gero, masara da sauransu.
Ya bawa matasa sama da guda dari injin cira da fitar da kudi (POS) tare da da koya musu sana’ar kuma da ba su jarin Naira dubu 50 kowannensu. Hakazalika, akwai kashi na biyu na sana’ar POS da yake shiryawa wanda matasa sama da 400 zasu amfana kuma kowanne da jarinsa.
Baya ga waɗannan kuma, akwai ayyukan da Maigirma Sanatan Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattijai ta Tarayyar Nijeriya, Sanata Rufa’i Sani Hanga ya tsara zai aiwatar idan kasafin kuɗin bana ya fito ga su waɗanda kuma suke cikin daftarin kasafin kuɗin shekarar 2024 na cewa duk lokacin da gwamnatin tarayya ta saki kudi za a yi su. Wadannan ayyuka ga su kamar haka: gina ajujuwan makaranta a garin Gunduwawa da ke yankin ƙaramar hukumar Gezawa; gina wasu ajujuwan a ƙaramar hukumar Warawa; gina wasu ajujuwan a Makarantar Sakandiren ‘Yan Mata ta Dakata; gina ajujuwa ajujuwa a Makarantar ‘Yan Mata ta Tsamiyar Zubau da ke karamar hukumar Dala; gina ajujuwa a Kadawa da ke ƙaramar Hukumar Ungogo; gina ajujuwa a Islamiyyar Abdullahi Sani Makarantar Lungu da ke Fagge D2; gina ajujuwa Makarantar Islamiyya da ke Satatima a yankin karamar hukumar Birni.
Akwai kuma koyawa matasa da mata sana’ar kiwon kifi ta zamani, rabon kayan koyo da koyarwa a wasu makarantun da ke yankin Kano ta Tsakiya; rarraba kayan makarantar Islamiyya a wasu fadin yankin Kano ta Tsakiya; gina cibiyar horar da mata a karamar hukumar Dala; gina titi da babban titin Zariya ya shiga cikin garin Garin Babba da ke karamar hukumar Garun Mallam; samar da kayan koyo da koyarwa da kayan makaranta ga daliban da ke makarantar Islamiyyun dake dukkanin yankin kananan hukumomi 15 da yake wakilta; samar da baburan hawa ga ‘yan asalin mazaɓarsa; samarwa da kuma sanya fitilun kan titi masu amfani da hasken rana; gina titi tun daga karamar hukumar Ungogo har zuwa ƙaramar hukumar Minjibir.
Tun yana kamfen ya debi matasa da dama ya kuma koya musu sana’oin hannu iri daban-daban wanda yanzu haka jira ake gwamnati ta saki kuɗi daga cikin kasafin kuɗin wannan shekarar a ba su kayan sana’ar; ya zaga kowace ƙaramar hukumar da ke yankinsa ya yi gyaran burtatsai saboda wahalar ruwa; shi ne ya fara yi wa kowacce ƙaramar hukumar ta da ke Kano ta Tsakiya samar da magunguna kai tsaye ga jama’a na gargajiya inda al’umma suka ji daɗi suka kuma gode.
Ya kai ƙuduri akan samar da Jami’ar Gona a ƙaramar hukumar Kura; ya kai ƙuduri akan gine-gine da ake yi a magudanan ruwa wanda hakan ne ke kawo ambaliyar ruwa; ya kai kuduri majalisa akan samar da makaranta a jihar Kano wacce za ta yi yaƙi da masu shaye-shayen miyagun kwayoyi; ya kai kudiri akan hukumar kiyaye hadurran kan titi ta kasa; sannan ya taimaka wajen ƙudurori da suka wuce da dama duk da suka wuce.
Baya ga waɗannan ayyuka da muka lissafa, wadanda a zahiri jama’a sun shaida su, ga kuma wasu daga cikin ayyukan da Mai Girma Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Rufa’i Sani Hanga yake shirin gabatarwa ga yankinsa da yake wakilta a Majalisar Dattijai ta ƙasa, wato Kano ta Tsakiya idan aka saki kuɗi daga cikin kasafin kuɗin shekarar nan su ne kamar haka:
Daga cikin ayyukan dai akwai gina titin Layin Makabarta a yankin da ya hada kananan hukumomin Kumbotso da Nassarawa; samar da kayan koyo da koyarwa a dukkanin mazabu 172 da ke yankunan kananan hukumomi 15 da yake wakilta; siya da rabawa daliban makarantun firamare kekunan hawa da ke yankin Kano ta Tsakiya; gina titi daga Layin Chairman zuwa Firamaren Maikalwa a yankin karamar hukumar Kumbotso; samar da baburan hawa ga wasu mutanen a yankin Kano ta Tsakiya.
Gina sababbin ajujuwa da gyara wasu a makarantun firamaren da suke cikin kananan hukumomi 15 na Kano ta Tsakiya. Gina titi tun daga Sallari Gidan Inuwa mai mai har zuwa Babban Giji Layin Mai Unguwa Tela a yankin karamar hukumar Tarauni. Gina tituna a wadannan wurare kamar haka: titin St. Louis da ke kan titin Dantata a karamar hukumar Nassarawa; Titin Maikalwa zuwa Gurungawa a karamar hukumar Kumbotso da kuma titin Layin Mai Allo zuwa Makarantar Firamaren Mariri.
Sayen tiransfoma da dasata a wasu yankunan da ke cikin Kano ta Tsakiya; samar da kekunan dinki domin rarraba su a shirinsa na samar da ayyuka da sana’o’i ga mutanensa a wasu kananan hukumomi da ke yankin Kano ta Tsakiya.
Ayyukan suna da yawa matuka da gaske, kuma fa duk da haka, sai da ya shafe kusan watanni takwas (8) yana fama da jinya a gida da kasar waje, amma duk hakan bai hana Sanata Hanga gudanar da ayyukansa na alheri ba ga yankinsa, na baya-bayan nan shi ne wanda ya sha suka daga wasu gungun makiya marasa son cigaban dan Adam, shi ne lokacin da ya raba tukwane da likkafani da kuma motocin daukar gawa. Ko shakka babu, wannan aiki ne mai girma wanda wasu jihohin ma tuni sun kwaikwayi irin wannan aikin alheri, kuma an ga alfanunsa. Idan zan iya tunawa, akwai wani shahararren masallacin juma’a a yankin karamar hukumar Gwale, kusan sallar juma’a biyu na ji suna neman tallafin likkafani saboda ana yawan zuwa masallacin nemansa kuma babu. To idan irinsu Sanata Hanga ba sa irin wannan hangen nesan haka za a rika rufe matattu babu likkafani kenan?
Toh ya Ilahi masu adawa da Sanatan Kano ta Tsakiya mai suke nufi ne? Mai suke so ya yi musu? Duk wadannan ayyukan fa an yi su ne kuma an samar da wadanda za ayi duk cikin shekara daya da hawansu mulki. Haka zalika duk cikin shekara dayan nan, ya kwanta jinya kusan wata 8 yana asibiti an yi masa aiki. Toh in dai ba makiya Kano ta Tsakiya ba ko kuma masu son kansu a fito a gaya mana wani Sanata ne a tarihi ya taba irin wannan ayyukan cikin shekara daya kacal? Banda aiki da ya samarwa mata na ‘yan sanda, ciɓil defence da sauransu. Banda alkhairai da yayi a gefe. Babu shakka mun yi imani yanzu duk masu adawa da Sanata Rufai Hanga ba shi suke wa adawa ba, makiya Jihar Kano ne kuma basu son bukatar kansu kawai ta biya.
Irin waɗannan ayyukan irinsu ake bukata, kuma ina jan hankalin Maigirma Sanata da kada irin wannan farfaganda da makiya da ‘yan adawa ke ci gaba suke yada wa su dauke hankalinsa daga irin ayyukan da yake yi wa al’ummarsa. Kullum muna roko da addu’ar Allah Ya kara wa Sanata lafiya ya cigaba da ayyukan alherin da yake yi wa al’ummarsa su cigaba da morar romon dimukaraɗiyya ta hanyar kyakkyawar wakilcinsa.
Kankarofi yana zaune ne a unguwar titin zuwa Fadar Mai Martaba Sarki, Kano
