Atiku ya caccaki masu yunƙurin daƙile cigaban matatar Ɗangote

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi gargaɗi kan yunƙurin da wasu mutane na ciki da na waje ke yi na kawo cikas ga cigaban matatar man Dangote.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a akn shafinsa na ɗ a ranar Asabar, Atiku Abubakar ya bayyana matatar a matsayin wani muhimmin aiki na kamfanoni masu zaman kansu da aka sanya don biyan buƙatun gida da waje.

Ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su tabbatar da cewa mutanen gida da na waje ba su hada kai don hana wasar cin moriyar matatar man ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Kowane iyaye da ke jiran isowar yaro za su ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa reno da ci gaban, wannan albarka mai daraja ya kasance babban abin da aka fi mayar da hankali a kai. Wannan wa’idar ta shafi daidai da saka hannun jari, ko na cikin gida ne ko na ƙasa da ƙasa.

“Da wannan fahimtar, na yi taka-tsan-tsan wajen yin la’akari da duk wani yunƙuri na ganganci na kawo cikas ga ci gaban matatar dangote, wani muhimmin aiki na kamfanoni masu zaman kansu da aka tanadi don biyan buƙatunmu na makamashi da kuɗin waje.

“Tare da ‘yan ƙasa da dama na fatan alheri, ina kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su ɗauki tsattsauran mataki don tabbatar da cewa sojojin ciki da na waje ba sa haɗa kai don hana mu cin gajiyar alfanun da aka yi mana alƙawari na wannan yunƙuri na kawo sauyi.”

By ukarofi