Shettima ya yaba wa MTN bisa gudunmawar tallafin Biliyan ɗaya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yaba da gudunmawar Naira biliyan 1 ga shirin tallafin abinci na gwamnatin tarayya da na’urorin zamani guda 4,600 domin raba wa makarantu da babban kamfanin sadarwa na MTN ya bayar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugaban kamfanin sadarwa na MTN na Nijeriya, Ernest Ndukwe a ziyarar ban girma da ya kai fadar shugaban ƙasa.

Ya ce, matakin da kamfanin na MTN ya ɗauka na ƙoƙarin da gwamnati ke yi na magance wahalhalu a ƙasar nan ya dace a yi koyi da shi kuma yana nuni da yadda yake ƙoƙarin bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.

“Ina matuƙar alfahari da gudunmawa da kuma jajircewar ku ga cigaban ƙasarmu. A madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ina so na gode muku kan wannan karimci,” inji shi.

By ukarofi