Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ɗan rajin kare haƙƙin bil’adama, Omoyele Sowore, ya caccaki gwamnatin jihar Kano bayan wata sanarwa da ta fitar cewa masu zanga-zanga sun sace fayil ɗin shari’ar cin hanci da rashawa na tsohon gwamnan jihar, Umar Ganduje.
Sowore ya ce bai kamata wannan furuci ya sa a ci gaba da shari’ar tsohon gwamnan jihar Kano ba, wanda a halin yanzu shi ne shugaban riƙo na jam’iyyar APC na ƙasa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, wanda ya kai ziyara a kusa da babbar kotun jihar a ranar Larabar da ta gabata, ya koka kan yadda masu aikata laifukan zanga-zanga suka lalata gine-ginen baki ɗaya tare da wawashe dukiyoyin da suka kai Naira biliyan 1.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya raba wa manema labarai a Kano.
“Abin takaici ne matuƙa yadda maƙiya jihar Kano suka ɗauki hayar wasu da ba a so su lalata daya daga cikin gine-ginen jama’a mai ɗimbin tarihi da nufin daƙile tuhume-tuhumen da ake yi wa Ag. Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje, da iyalansa da mataimakansa,” in ji sanarwar.
Sai dai a martanin da Sowore ya mayar, ya ce za a iya kwatanta furucin da gwamnatin jihar Kano ta yi da kalaman Gwamna Babajide Sanwo-Olu na cewa an ƙona fayil ɗin cin hanci da rashawa na Shugaba Bola Tinubu a lokacin zanga-zangar Endsars na 2020.
A nasa ɗ, a ranar Laraba, Sowore ya ce, “Ya kamata su sami kwafin Bello Galadanchi wanda aka fi sani da ɗan Bello). Don haka, shin duk takaddun tare da kotuna kaɗai, kuma babu kwafi tare da masu bincike, lauyoyi, da masu gabatar da ƙara?
“Na tuna da yadda gwamnatin jihar Legas ta ce an kƙona fayilolin cin hanci da rashawa na Bola Tinubu a lokacin #EndSARS.”
