
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta gayyaci shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero kan zarginsa da hannu acikin ɗaukar nauyin ta’addanci da wasu laifukan da suka shafi sata.
Cikin wata sanarwa da Mataimakin Kwamishinan ƴan sanda, IRT ya fitar, rundunar ta umarci Ajaero ya hallara a ofishin IRT a ranar Talata 20 ga watan Agusta.
Sanarwar ta ce, “wannan ofishin na bincike kan laifukan makircin fashi, ɗaukar nauyin ta’addanci, zamba cikin aminci, maƙarƙashiya da sata ta yanar gizo waɗanda aka ambaci sunanka.”
Rundunar ta kuma yi gargaɗin cewa, za a kama shi matuƙar ya ƙi amsa wa kiran da aka masa.
