MAKAMASHI: Son zuciya ɓacin rai

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Daga cututtukan zuciya guda 360 da malaman falsafa suka fitar, sun tabbatar da cewa, babban cikinsu shine “son zuciya”, mabiyansa shine, “ƙin gaskiya”. A cewarsu, dalilin sanya son zuciya daga farko domin yana faruwa ne daga jahilcin abin nan da ita zuciya ta ke so, suka ce jahilci babban ciwo ne wanda ba shi da magani illa ilimi, ga shi kuma, shi ilimi kattarabu ne, wato turɓaya ne ko kuma mu ce kumfar teku ne. Mun kwararo wanna shimfiɗa ne domin yin tambihi kan zanga-zanga raka gudanar daga ɗaya ga wannan wata na Agusta, 2024, zuwa ga 10 ga watan.

Bincike na harshen Hausa ya nuna cewa, zanga-zanga sabuwar kalma ce da kakakin yaɗa labarai suka zo da ita, kuma su ka yaɗa ta a cikin al’umma, kalmar da Bahaushe ya sani ita ce rikici, bore, hayaniya da kuma tawaye. Bahaushe ya na amfani da su, domin nuna matsayin abubuwan da suke faruwa a daidai wannan lokaci. Idan yaro kuma mu ce jinjiri da bai wuce shekara biyu ba, aka same shi yana koke-kokena rashin dalili. A wannan guri ne, ake amfani da kalmar rikici, domin babu tabbas mai ya haifar da wannan ɗabi’a.

Da takarda ta ɓarke tsakanin mutum da mutum ko tsaknin mutum da matarsa ko kuma tsakanin dangi da dangi ko gari da gari ko tsakanin kabilu ko addinai, rashin sanin musabbanin wannan fitina sai a kira ta da rikici. Haka idan fitinar ta yi tsanani har dalilin farko na finan ya haifar da wasu fitunu, wannan matsayi ya koma rikici kamar abubuwan da suke faruwa tsakanin Yahudawa da Falasɗinawatare da ƙungiyar Hamas. Kuma rikici yake faruwa a Sudan da Siriya wato Sham da kuma rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a Mauritania da kuma Western Sahara (Sadar).

Malam Bahaushe ya daɗe da sanin bori domin kuwa yana daya daga cikin daɗaɗɗun, ɗabi’u da Bahaushe yake amfani da shi wajen halin da yake ciki. Domin kuwa akwai ’yan tawaga ta musamman ta nuna halin da mutum yake ciki domin samar da magani mutum mai hankali, nutsattse, amma idan ana buƙatar sai a kaɗa masa taken wannan borin duk wanda yake da da’awar wannan borin sai ya hau. Akwai masu cewa, bori shine addi na farko da Bahaushe  ya gada kaka da kakanni kafin shigowar addinin Musulunci da addinin mishan su shigo ƙasar Hausa.

Bayi da talakawan ƙasa na yi wa shugabanninsu bore kan wani al’amari da talakawan suka ga rashin adalci a gare su. Rashin adalci da kyautatawa suke sawa a yi bore ga shugabanni. Boren yana tsayawa ne ga shugabanni kawai, shi ma yana tsayawa ne ga rashin ɗaukar umarni na a yi ko a bari. Wannan ta sa babu wata sikira a tarihi da take nuni da cewa shugaba (sarki) kaza jama’arsa sun yi masa bore, saboda wani dalili wanda ya sha musu kai.

Boren farko a cikin tarihin wannan yanki na Arewa shine tarzomar da matan Tibi suka gudanar a shekara ta 1963, wanda shi ya samar da ’yan sandan kwantar da tarzoma a ƙasar nan ƙarƙashin jagorancin Sufaitan ’Yan Sanda Baban Kowa, mutumin ƙasar Ringim ta Jihar Jigawa. Haka Kanawa ba za su manta da tarzomar almajiran Malam Muhammadu Marwa Maitatsine na shekara ta 1980 da kuma tarzomar jita-jitar cire Sarkin Kano a 1982 ba.

Duk waɗannan misalai mun yi su ne a matsayin tarzoma. Ita tarzoma fitina ce, kamar tarzomar  almajiran Muhammadu Marwa Maitatsine an halaka mutane sama da rabin miliyan a Katsina, Bauchi, Yola, Jalingo, Maiduguri, Gusau da Birnin Sakkwato. Saboda haka, za mu kira zanga-zangar wannan wata na August, 2024 ita ce tarzoma ta farko da ta karaɗe dukkan ƙasa da sunan ‘’a dawo da cire tallafin man fetur’’ saboda matsaloli da ya haifar.

Maganar gaskiya dawo da tallafin man fetur annoba ce da ta fi annobar Korona da cutar mashaƙo ta kowa ya zauna a gida, duk da tsananin fatara da talauci ya mamaye ƙasa, amma biyayya ga shugabannin ƙasa, sai aka samu waraka. Haka da ’yan Najeriya sun yi biyayya ga gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, wanda ya fi su gaskiya da kirarinsa ‘’no going back’’ wajibi ne ga duk ɗan ƙasa na gari ya bayar da goyon baya ɗari-bisa-ɗari.

Da ’yan Nijeriya na bibiyar tarihi, da za su manta da mutuwar Shugaban ƙasa Sir Tafawa ɓalewa da Janar Murtala Ramat Muhammad  da Janar Sani Abacha  da kuma Shehu Musa ’Yar’Adu’a. Dukkansu sun bayar da tasu gudunmawar wajen gina wannan ƙasa.

Ka amfana kai tsaye ko kuma a kaikaice ka amfana duka ɗaya ne, domin kuwa haka rayuwa take.

Idan za mu buga misali da wannan lokacin na Shugaba Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima Mustapha za ka tarar wasu ’yan Najeriyar sun fi samun kwanciyar rai sama da duk wani shugaba daga 1960 zuwa yau ta fuskar tattalin arziki da walwala. Wasu kuma asara suka tafka ta rakukan ’yan uwansu da kuma dukiyoyinsu. Ita duniya juyin ‘yar masa take, wato dai kamar rawar ’yan mata ta gaba ta koma baya.

Saboda haka idan ka na so ka cimma ribar shugaba da ke kan mulki, saurare shi da idon basira, mane ne burinsa na mulki, “policy” shi ya zo da burin cire tallafin man fetur, wanda shugabannin baya suke bayarwa. Idan muka lura wasu ’yan ƙasa sun ci moriyar wannan dama, don haka raba su da wannan garaɓasa zai taɓa rayuwarsu, saboda za su yi iyakar ƙoƙarin su ga ba a tamkwaɓe daular da suke ciki ba. Hanya ta farko ita ce shiryawa wannan zanga-zanga wacce ta juye ta koma tarzoma har ta kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Hassada (enɓy) a siyasa ta dimokraɗiyya ba ta da gurbi domin dama an tsara ku biyu, uku, huɗu har zuwa biyar ka na neman kujera ɗaya, saboda haka ka ci ko ka faɗi. Idan ka faɗi sai ka taya wanda ya ci murna da yi ma sa fatan alheri. Daga nan sai ka sa ido idan ya cika alƙawari sai ka yaba masa, idan kuma ya gaza alƙawarin da ya ɗauka sai soke shi, kai kuma ka kawo taka dabarar da ka ke ganin ita ce mafuta. Idan cire tallafi ya yi tsanani sai ka kawo dabarar ba tarzoma da fushi ba.

Shirya tarzoma a ƙasa, laifi ne babba domin raba ’yan ƙasa ya ke yi wanda zai iya raba ƙasar bakiɗaya. Mu na gani a yanzu a Sudan da Siriya da kuma Yamani. Saboda haka a hukunta dukkan waɗanda  suka shirya wannan kitimirmira. Mu sani son zuciya ɓacin rai. Hamayya ba adawa ba.

By ukarofi