NIMET ta yi hasashen samun tsawa da mamakon ruwan sama a Najeriya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar kula da yanayi ta Ƙasa, NIMET ta ce ta yi hasashen za a samu tsawa da mamakon ruwan sama a faɗin Najeriya tsakanin ranakun Litinin da Laraba.

Hasashen da hukumar ta fitar a Abuja ya nuna za a samu tsawa a yankunan jihohin Kano, Katsina, Zamfara, Jigawa, Kaduna, Taraba da Bauchi a lokacin safiya.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuma, za a samu madaidaicin saukar ruwan sama a yankunan jihohin Neja, Nasarawa, Benue, Kwara, Abuja da kuma Filato.

A yammaci kuma za a samu tsaka-tsakin saukar ruwan sama haɗe da tsawa a wasu yankunan Abuja, Nasarawa, Filato da kuma Kogi.

Haka nan, ya nuna za a samu saukar tsaka-tsakin ruwan sama a yankunan jihohin Kudanci da su ka haɗa da; Osun, Oyo, Ekiti, Ebonyi, Enugu, Anambara, Cross-River, Ribas, Delta, Bayelsa da Akwa-Ibom da yardar Ubangiji.

By Babaji