
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce tun da ya karɓi ragamar shugabancin Najeriya ya fara yunƙurin dakatar da ayyukan rashawa ta hanyar bai wa hukumomin EFCC da ICPC isassun ƙuɗaɗe da kuma ƙauracewa sanya baki acikin ayyukansu.
Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Litinin inda ya bayyana rashawa a matsayin ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da ke daƙile cigaba a ƙasar, ya na mai cewa wajibi ne a hukunta duk wanda aka samu da hannu acikin laifin.
Shugaban wanda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi a taro cibiyoyin harkokin rashawa na yammacin Afirka karo na shida a Abuja, ya ce rashawa wani jigo ne da ke dakatar da cigaba da samun alheri ga ƙasashen yankin.
A matsayinsa na shugaban ECOWAS, Tinubu ya nemi ƙasashen da ke ƙarƙashin ƙungiyar su haɗe kai wajen inganta harkokin hukumomin yaƙi da rashawa don amfanin kansu da al’ummarsu.
A lokacin da ya ke jawabi, Ministan ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, Yusuf Tuggar ya ce ƙasashen Afirka su kan rasa jimillar Dala biliyan 8.6 a duk shekara sakamakon ɓarnata dukiya, ya na mai cewa akwai buƙatar ECOWAS ta sanya hannu ga ƙoƙarin nahiyar wajen tabbatar da tsari kan gudanar da dukiyar al’ummarsu da ƙasashensu.
